FG ta amince da bude sabbin kwalejin kimiyya da fasaha a jihohi 16

FG ta amince da bude sabbin kwalejin kimiyya da fasaha a jihohi 16

Gwamnatin tarayya ta aminta da gina sabbin kwalejin kimiyya da fasaha a jihohi 16 na kasar nan. Ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin jawabinsa a taro na 64 na kungiyar ilimi ta kasa da aka yi a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.

Adamu ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya na kokarin gani ta samar da ingantaccen ilimi a sashi daban-daban na fadin kasar nan.

Ministan ya kara da cewa, gwamnatin tarayya na kokarin ganin ta habaka tsarin ilimi don samar da hanyoyin dogaro da kai ga 'yan kasar nan.

Ya ce: "Babu shakka, ilimin kimiyya da koyon sana'a su ne jigo na habakar duk wasu masana'antun kasar nan. A don haka ne za a iya shawo kan rashin aikin da ya addabi matasa matukar an basu ilimi mai nagarta kuma na dogaro da kai."

"Koyar da sana'o'i da kuma horar da matasa a duk fadin duniyar nan shine jigo a tsarin fatattakar rashin aikin yi. A kokarin mu na ganin an samu ilimin dogaro da kai, an bada muhimmanci ga ilimin fasaha, koyon sana'o'i da aiyuka don dogaro da kai,"

DUBA WANNAN: Wata mata ta kashe jaririn da ta haifa a Kano

A yayin bude taron, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, yace, kasar nan zata iya kaiwa matakin cigaba ne idan an inganta 'yan kasar da ilimin da ya dace da kuma sana'o'in da zasu kawo cigaba ga kasar baki daya.

Gwamnan yace: "Zancen gaskiya shine, babu kasar da zata zama daidaituwa ta bangaren siyasa, tattalin arziki da wayewa ba tare da an habaka 'yan kasar da sana'o'in da zasu inganta rayuwarsu ba kuma su taka rawar gani wajen kawo cigaban kasar."

Hakazalika, ministan harkokin mata, Pauline Tallen ta jinjinawa Gwamna Wike akan kokarinsa na inganta karatun yara mata a jihar. Tace, ilimantar da 'ya'ya mata zai bunkasa gida tare da kasar baki daya.

Tallen tayi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su kokarta wajen ilimantar da 'ya'ya mata. Tallen tace, ma'aikatar harkokin mata zata hada guiwa da ma'aikatar ilimi don bunkasa ilimin 'ya'ya mata a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel