Dangote: Kwanan nan Najeriya za ta fara fita da shinkafa ketare

Dangote: Kwanan nan Najeriya za ta fara fita da shinkafa ketare

Kamfanin Dangote na Duniya, ya yi alkawari cewa labarin Najeriya zai tashi daga matsayin kasa mai shigo da shinkafa zuwa kasar da ke fita da shinkafa zuwa kasashen Duniya kwanan nan.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, Dangote ya sha alwashin ganin Najeriya ta daina dogara da kasashen ketare wajen abincin ta. Kamfanin ya bayyana wannan ne ta bakin Kunt Ulvmoen.

Mista Kunt Ulvmoen, wanda shi ne babban Darektan Kamfanin ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taro da aka yi da ‘yan kasuwa a ranar musamman da aka ware a matsayin ranar Dangote.

Kamfanin ya ware filin noma har eka 150, 000 domin noman shinkafa a jihohin Jigawa, Kano, Kebbi, Nasarawa, Neja, Sokoto da kuma Zamfara. Wannan zai taimakawa burin gwamnatin kasar.

KU KARANTA: An daina satar kudin man fetur da zuwan Buhari - Ribadu

Bugu da kari kamfanin na kokarin kafa wuraren casa wanda za su taimaka wajen samar da akalla tan miliyan guda na shinkafa a duk shekara. Wuraren casa goma za a bude a fadin Najeriya.

Ulvmoen ya ke cewa Dangote aka sani da shinkafa a Najeriya kafin su daina. An yi wannan taro ne a kasuwar bajakolin Duniya a Garin Legas, wanda wannan shi ne karo na 33 da aka taba yi.

Dangote sun daina shigo da shinkafa daga waje ne domin ganin an taimakawa mutanen cikin gida. Sai dai har gobe mutane su na neman shinkafarsu a kasuwa don haka za su koma sana’ar.

Darektan na katafaren Kamfanin ya ce dole su shiga noman shinkafar da aka sansu da su a da. Za su rika noma shinkafa ton miliyan guda wanda za a gyara har ta kai ana fitar da ita zuwa waje.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel