Wata jami'a ta sallami malamai 8 akan laifin lalata da dalibai

Wata jami'a ta sallami malamai 8 akan laifin lalata da dalibai

Jami'ar jihar Akwa Ibom, ta kori wasu malamanta 8 akan laifin cin zarafin dalibai da ta kamasu da shi.

A yayin tattaunawa kana batun a jiya a Ikot Akpaden, daga karamar hukumar Mkpat Enin ta jihar, shugaban jami'ar, Farfesa Eno Ibanga, yace an kori malaman ne saboda lalata da dalibai mata da aka kama hannunsu dumu-dumu ciki.

Farfesa Ibanga yace, wasu daga cikin matsalolin na gaban kotu. Ya kara da cewa, hukumar makarantar ta cafke dalibai 10 da ta kama da laifin kafa kungiyar asiri.

Ya ce an kama daliban ne dauke da wata karamar akwatin saka gawa da gatari a wani wuri da ke cikin jami'ar a hanyarsu ta zuwa wurin rantsar da su a kungiyar tsafin, kuma dukkansu na sanye da jajayen tufafi.

A cewarsa, jami'ar na iya bakin kokarinta wajen ganin ta tabbatar da da'a a tsakanin lakcarori da dalibai, tare da bayyana cewa hukumar makarantar kan gudanar da cikakken bincike, duk lokacin da aka samu wata matsala, kafin ta dauki matakan ladabtar wa.

DUBA WANNAN: Jiya ba yau ba: Jarumi Shah Rukh Khan ya cika shekaru 54 a duniya

"Mun sallami malamai da ke koyar wa guda takwas saboda samunsu da laifin lalata da dalibai da kuma karbar nagoro a hannun dalibai.

"A yanzu haka zancen da nake muku akwa malamin da ake gudanar da bincike a kansa, kuma ina mai tabbatar muku cewa ba zai tsallake ba, sai ya fuskanci hukunci.

"Akwai wasu da yanzu haka suna kotu ana tuhumarsu. Na yi rantsuwa a kan cewa zan gudanar na mulki na gaskiya da zai kawo tsafta a yadda ake gudanar da harkoki a wannan jami'a," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel