Zanga-zanga: Kungiyoyi 20 na Mata zalla sun mamaye majalisar dokokin jihar Kano

Zanga-zanga: Kungiyoyi 20 na Mata zalla sun mamaye majalisar dokokin jihar Kano

Wata tawagar wakilan kungiyoyi 20 na mata zalla sun yi dandazo a majalisar dokokin jihar Kano domin gudanar da zanga-zangar neman mambobin majalisar su shiga maganar yaran nan guda 9 da aka gano a jihohin yankin kudu maso gabas bayan an sace su daga Kano.

Kungiyoyin matan a karkashin hadakar kungiyar da Ulama da sauran kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) sun bukaci majalisar ta kafa kwamitin bincike na musamman a kan lamarin.

Shugabar wakilan kungiyoyin, Amira Shitu Abdulwahab, ta ce sun zo majalisar ne domin rokon ta kafa kwamiti da zai gano wurin da dokar jihar ta samu rauni da har wasu 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka a jihar.

Amira ta bayar da shawarar cewa ya kamata majalisar ta daukin gagga wa da zarar ta gano inda dokar ke da rauni domin kawo karshen matsalar baki daya. Shugabar ta ce kamata ya yi dokar kashe masu garkuwa da mutane da gwamna Ganduje ya kirkira ta hada da masu satar yaran.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi talauci a Najeriya

"Mu na kira ga majalisa a kan ta kirkiri wata doka zata tilasta gwamnatin jiha ta bawa hukumomin tsaro dukkan goyon baya da tallafin da suke bukata domin gano ragowar yaran da aka sace da kuma dawo da su hannun iyayensu.

"Ya kamata majalisa ta yi dokar ake kulle duk wani gida da aka samu ana amfani da shi wajen boye mutanen da akai garkuwa da su, sannan kuma a tuhumi mai gidan.

"Sannan muna kira ga wannan majalisa a kan ta umarci gwamnatin jihar Kano ta janye wakilcin da 'yan kabilar Igbo da kungiyar Kiristoci (CAN) ke da shi a gwamnatin jihar saboda bamu ga wata fa'idar shigo da su cikin harkokin da suka shafi jihar Kano kawai ba," a cewar ta.

Da yake mayar martani ga wakilan kungiyoyin matan, shugaban majalisar jihar Kano, Alhaji Abdulazeez Garba Gafasa, ya yaba wa matan a kan matakin da suka dauka na zuwa majalisar domin gabatar da korafinsu.

Kazalika, ya dauki alkawarin cewa mmajalisar zata dauki mataki domin kawo karshen lamarin da kuma kirkirar dokokin da zasu tabbatar da kare hakkin mata da kananan yara.

NAN

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel