2019: An binciko babban abin da ya sa Atiku ya ke makale a Dubai har yanzu

2019: An binciko babban abin da ya sa Atiku ya ke makale a Dubai har yanzu

Idan ku na biye da labari, za ku san cewa ‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya dauke kimanin watanni shida ya na birnin Dubai da ke kasar UAE tun cikin Watan Afrilu.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta yi bincike game da abin da ya sa Alhaji Atiku Abubakar ya tare a kasar Larabawan tun bayan kammala zaben bana inda ya sha kashi a hannun jam’iyyar APC.

Binciken da jaridar ta yi ya nuna cewa Atiku Abubakar ya labe ne a kasar UAE domin gujewa yunkurin da wasu manya a gwamnati da jam’iyyar APC su ke yi na jefa shi cikin wani tarko.

Wani daga cikin Makusantan ‘dan takarar shugaban kasar ya tunatarwa jama’a cewa: “Abubuwa sun yi zafi bayan zaben 23 ga Fubrairu ta fuskar karfin jiki da tunani da ruhi da sauransu…”

Wannan Bawan Allah ya cigaba da yi wa ‘yan jarida bayanin cewa: “…Wannan ya sa ya dauki lokaci domin ya je ya huta. Dukannin mu mun yi wannan. Ni ma haka (na tafi na huta).”

KU KARANTA: Yadda Najeriya ta ci ribar zaman Buhari da Yariman Saudi

Shi kuma wani na kusa da babban ‘Dan siyasar ya fadawa Manema labarai cewa: “Ya dauki lokaci ya huta ne bayan zabe, amma ya yi niyyar dawowa domin ya halarci wani biki da aka yi a AUN.”

Wannan mutumi wanda bai bari Manema labarai sun kama sunansa ba, ya yi bayani cewa Atiku ya shirya halartar wannan taro da aka yi Jami’ar AUN a Watan Mayu, sai kuma tafiya ta kama sa.

Mun samu sahihin bayanin mugun shirin da wadanan mutane su ke kitsawa. Su na kokarin yi masa abin da aka yi wa MKO Abiola ne. Duk mun san abin da ya faru da MKO Abiola a baya…”

“…Inda aka yi kutun-kutun, aka zarge shi da laifi, aka damke sa, da sauransu, don haka ya ja baya. Har gobe wannan bai canza ba, mun san halin wadanda ke rike da mulki da abin da za su iya…”

“…Kuma ba za mu so ya zama abin labari ba. Maganar ita ce tsarin damukaradiyya ne yake kan siradi. Wannan shiyasa ya ja jikinsa yayin da ake wannan.” Majiyar tace shiyasa ya ke Dubai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel