Bidiyo: Yadda aka nuno tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana rakashewa a wajen wani biki

Bidiyo: Yadda aka nuno tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana rakashewa a wajen wani biki

- Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Instagram ya nuna yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yake cashewa a wajen wani taro

- An nuno tsohon shugaban kasar yana rawa bayan an sanya wata wakar Yarabawa da tayi masa dadi

- Tsohon shugaban kasar dai yana daya daga cikin manyan mutane da suka samu damar halartar wannan taro a kasar Amurka

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda yake daya daga cikin manyan baki wajen taron bude bankin cigaban nahiyar Afrika wato 'Africa Development Bank (AfDB)' a turance, an hango tsohon shugaban kasar dai yana cashewa a wajen wannan taro da aka gabatar a kasar Amurka.

Jakadan Quinn, shugaban gidauniyar bada kyautar abinci ta duniya shima ya samu damar halartar wannan taro a kasar ta Amurka.

Akinwumi Adesina wanda ya wallafa wannan bidiyo a lokacin da tsohon shugaban kasar yake rawa ga wata wakar Yarabawa da aka sanya a wajen taron yayi rubutu a kasa kamar haka:

KU KARANTA: An samu wata tsohuwar Nokia 3310 da caji 70% bayan shekara 20 tana kunne a ajiye

"Rawar shugabannin kasa, muna godiya kwarai da gaske ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya samu damar halartar wannan taro namu, a yayin da ni da matata muka bude gidauniyar yaki da yunwa ta duniya mai suna 'World Hunger Fighters Foundation a Iowa cikin kasar Amurka.

"Haka kuma muna godiya ga Ambasada Quinn, shugaban gidauniyar bayar da kyautar kayan abinci na duniya, mun gode kwarai da gaske."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel