Ina ji ina gani haka 'yan sanda suka dinga bi da bi a kaina suna zina dani saboda bani da cin hancin da zan ba su - In ji wata budurwa

Ina ji ina gani haka 'yan sanda suka dinga bi da bi a kaina suna zina dani saboda bani da cin hancin da zan ba su - In ji wata budurwa

- Wata budurwa ta bayyana dalla-dalla yadda wasu 'yan sanda suka tare ta a cikin birnin Abuja suka yi mata fyade

- Budurwar ta ce sun yi mata fyaden ne saboda ba ta da cin hancin da za ta ba su

- Ta kara da cewa a lokacin da suka tare ta duk ta rude ta rasa me tayi musu da yasa suka tare ta har ma suke binciken ta

Wata budurwa da ta fada tarkon 'yan sanda wacce aka boye sunanta saboda tsaro ta bayyana yadda 'yan sanda suka yi mata fyade saboda bata da kudin da za ta basu a matsayin cin hanci.

Budurwar a wata hira da aka yi da ita ta bayyana cewa ta rude ta kuma rasa me zata yi bayan 'yan sandan sun kama ta a Abuja.

Wannan labari dai wata ce mai suna @ukejeihuoma ta wallafa shi a shafinta na Twitter, inda ta rubuta kamar haka:

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Hafsat Shehu tsohuwar matar Ahmad S Nuhu ta yi auren bazata

"Wannan budurwar da sauran 'yammata irinta suna bukatar abi musu hakkin su. Wata budurwa ta bayyana yadda wasu 'yan sanda guda hudu suka tsayar da ita a kan titi, inda har daya daga cikinsu yayi amfani da ita ba tare da ya sanya kwaroron roba ba.

"Saboda sun tsayar da ita a wajen da suka fito aiki, sai ta rude ta rasa menene tayi to sai ta fara tambayar su shin menene ya sanya suka tsayar da ita suke bincikarta.

"Maimakon su bata amsa sai ma suka fara cin zarafinta."

Yanzu haka dai anyi iya bakin kokari domin a samu a tuntubi hukumar 'yan sanda dangane da wannan lamari amma lamarin ya ci tura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel