Da dumi dumi: Kotun daukaka kara ta fatattaki dan majalisar APC daga jahar Bauchi

Da dumi dumi: Kotun daukaka kara ta fatattaki dan majalisar APC daga jahar Bauchi

Kotun daukaka kara dake zamanta a garin Jos ta sutale wani dan majalisa daga jam’iyyar APC, Alhaji Garba Muhammad Gololo daga kujerar da yayi dare dare a kai bayan ta kamashi da laifin amfani da takardun karatu na bogi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia E.Igor ne ya yanke wannan hukunci a ranar Juma’a, 1 ga watan Nuwamba inda ya fatattaki Gololo daga majalisar wakilai, inda yake wakiltar mazabar Gamawa ta jahar Bauchi.

KU KARANTA: Da walakin goro a miya: Sanatoci sun fara neman kulla kyakkyawar alaka da Sadiya

Alkalin ya bayyana cewa kotun ta kama Gololo ne da laifin amfani da shaidar karatun digiri na bogi, Masters (MA), na bogi, kai hatta shaidar kammala bautan kasa na NYSC daya bayyana ma hukumar INEC don shiga zabe a shekarar 2019 duka na bogi ne.

Wani dan siyasa kuma abokin karawar Gololo daga jam’iyyar New Nigerian People’s Party-NNPP, Isa Muhammadu Wabu ne ya kalubalanci nasarar da Gololo ya samu a zaben 2019, inda ya zargi Gololo da amfani da takardun karatu na bogi, karatun da Gololo yake ikirarin ya yi a jami’ar jahar Legas.

Daga karshe Alkali E. Igor ya baiwa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC umarnin ta gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 90 masu zuwa.

A wani labarin kuma, wata kungiyar magoya bayan gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai mai suna Nasirriya sun bude wani ofishin yakin neman zaben El-Rufai a matsayin shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023 a garin Jos na jahar Filato.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel