Tashin hankali: Sacewa wata Bafulatana tunkiya ya saka ta sha alwashin kashe wanda ya dauke mata dabba

Tashin hankali: Sacewa wata Bafulatana tunkiya ya saka ta sha alwashin kashe wanda ya dauke mata dabba

- Wata Bafulatana ta sha alwashin kashe duk mutumin da yake da hannu a sace tunkiyarta wacce ba ta jima da haihuwa ba

- Bafulatnar ta bayyana cewa an sha sace mata dabbobi a lokuta da dama amma ba ta taba jin ciwo irin na wannan tunkiya da aka dauke mata ba

- Yanzu dai ta bayar da kwanaki hudu ko a dawo mata da tunkiyarta ko kuma a samu gawar mutumin da ya sace mata

Wata Bafulatana da ta fusata sakamakon sace mata dabba, ta sha alwashin kashe duk wanda ya dauke mata tunkiyarta mai jego matukar aka kwashe kwanaki hudu ba tare da an dawo mata da tunkiyar ba.

A tattaunawar da tayi da Freedom Radio, Bafulatanar ta bayyana cewa an sha yi mata satar dabbobi, amma babu satar da ta yi mata ciwo kamar wannan, inda aka dauke tunkiyar har da dan da ta haifa.

Haka kuma ta kara da cewa, barawon tunkiyar ya yi ta fakon ta ya bari har lokacin da ta fita unguwa ya shiga har cikin gidanta ya sanya wa tunkiyar igiya tare da yin awon gaba da ita.

KU KARANTA: Tirkashi: Ko Tsirara zaki saka hotona Wallahi sai an aure ni - Martanin Sadiya Kabala ga Jakadiyar tonon silili

Ta ce a baya an daukar mata dabbobi har sau 6, amma yanzu an dauke mata tunkiyar ne mai kama da Rakumi, a don haka a yanzu ba za ta hakura ba kamar yadda ta hakura a baya, tana mai cewa matukar aka yi kwanaki 4 ba a dawo da tunkiyar ba, to za a samu gawar wanda ya sace ta.

Idan ba a manta ba a jiya ne muka kawo muku rahoton yadda wata mata ta hadawa wata akuyarta da ta haihu bikin suna a jihar Kano, inda aka sha shagali aka rakashe duka saboda murnar haihuwar wannan akuya wacce take kira da suna Abida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel