An samu Jami'a ta farko a Najeriya da za ta fara yiwa saurayi da budurwa bulala idan aka kama su suna soyayya
- Wata jami'ar kudi dake jihar Ekiti ta bayyana kudurinta na daukar mataki akan samari da yammata masu soyayya a cikin makaranta
- Hukumar jami'ar ta Afe Babalola ta bayyana cewa za ta yiwa duk mace da namijin da ta kama suna rike hannu da sunan soyayya a cikin makaranta
- Ta bayyana hakan ne domin rage matsala ta zinace-zinace dake faruwa a makarantun jami'a na kasar nan
Wani sabon bidiyo a yanzu haka yana ta yawo a kafafen sadarwa, inda wani mutumi wanda ya bayyana cewa shi Malamin jami'ar Afe Babalola ne, ya ce yanzu haka hukumar jami'ar dake jihar Ekiti sun yanke hukuncin fara yiwa dalibai mace da namiji bulala idan aka kama sun rike hannun juna.
A bidiyon mutumin ya bayyana cewa wannan doka ta fito daga bakin mutumin da ya samar da wannan makaranta ne, ya ce:
"Mun samu umarni daga wanda ya samar da wannan makarantar. Duk wadannan 'yammatan da suke da al'adar yawo da samari ko kuma su rinka kama hannunsu suna yawo da su, idan muka kama ku kuna irin wannan abin zamu yi muku bulala, kuma dokar za ta fara aiki daga wannan daren.
KU KARANTA: Allahu Akbar: Kauyen da ya fi kowanne gari a duniya koyar da Al-Kur'ani mai girma
"Zamu kira wannan abu da suna 'Operation Koboko' kuma zamu fara daga yau 30 ga watan Oktobar 2019. Da ku nake 'yammata da samari masu soyayya a cikin makaranta.
Ga dai bidiyon abinda malamin ya ce a kasa:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng