Gwamna El-Rufai ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Kano a fadar gwamnati

Gwamna El-Rufai ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Kano a fadar gwamnati

Mai martaba Sarkin, Alhaji Muhammadu Sunusi II ya kai ziyara jahar Kaduna, inda ya samu kyakkyawar tarba daga wajen mai girma gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai a gidan Sir Kashim Ibrahim.

Legit.ng ta ruwaito Gwamna El-Rufai ne ya gayyaci Sarkin Sunusi domin ya gabatar da jawabi ga wasu matasa 18 dake cikin gajiyar tsarin horaswa a sha’anin mulki da gwamnan ya kirkiro mai taken Sir Kashim Ibrahim Fellows.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta aika ma yan gudun hijira takardar sallama daga wani sansani

Gwamna El-Rufai ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Kano a fadar gwamnati
Gwamna El-Rufai ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Kano a fadar gwamnati
Asali: Facebook

Sarki Sunusi ya isa jahar Kaduna da safiyar Alhamis, 31 ga watan Oktoba, inda ya gabatar da jawabi ga matasan a kan cin hanci da rashawa, muhimmancin ilimi da kuma hakkokin mata.

Haka zalika idan za’a tun, mun ruwaito muku cewa gwamnan jahar Kaduna ya bayyana shirinsa na sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana a wasu gidaje guda 3, 400 a kananan hukumomin Jema’a, Kubau da Kajuru.

Sauran ayyukan da gwamnan ya kuduri gudanarwa daga cikin kasafin kudin shekarar 2020 akwai sanya wuta mai amfani da hasken rana mai tsawon kilomita 2 a dukkanin mazabau 255 na jahar, sai kuma amfani da hasken rana a tashoshin tafstace ruwan sha dake Malali da Zari.

A wani labarin kuma, wata kungiyar magoya bayan gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai mai suna Nasirriya sun bude wani ofishin yakin neman zaben El-Rufai a matsayin shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023 a garin Jos na jahar Filato.

Shugaban Nasiriyya, Hajiya Nafisatu Omar ta bayyana cewa El-Rufai ya cancanci zama shugaban kasar Najeriya saboda mutum ne da baya nuna bambamcin addini ko kabilanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel