Kano ta Dabo tumbin giwa: An yi shagalin bikin sunan wata akuya da ta haihu a jihar Kano

Kano ta Dabo tumbin giwa: An yi shagalin bikin sunan wata akuya da ta haihu a jihar Kano

- Ana cewa Kano ta Dabo tumbin giwa yaro ko dame ka zo an fika, maganar haka take, domin kuwa wani abin mamaki ne ya faru a ranar Litinin dinnan da ta gabata

- Abinda ya faru kuwa shine, yadda aka yiwa akuya bikin suna kamar dia yadda ake yiwa mace idan ta haihu

- Anyi biki tare da raye-raye da kade-kade, sannan aka sanyawa dan akuyar da aka haifa suna Murtala

An shiryawa wata Akuya mai suna Abida mai shekara daya a duniya kasaitaccen bikin suna don taya ta murnar haihuwar da namiji a jihar Kano.

Mai Akuyar mai suna Rukayya Muhammad Lawal ‘yar Asalin jihar Zamfara dake zaune a Kano , tace dalilin da yasa ta shiryawa Akuyar tata bikin sunan a yau, ta shafe sama da shekaru Ashirin dayin Aure kuma ta haifi ‘ya’ya bakwai amma duk sun mutu babu wanda yayi saura hakan yasa ta sayi Akuya da ta yiwa lakabi da suna Abida, kuma Allah ya albarkace ta da haihuwar da Namiji ta Kuma saka masa suna Murtala a yayin bikin sunan da aka yi a ranar Litinin 28 ga watan Oktobar nan da muke ciki.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Daga yanzu 'yan Najeriya za su iya zuwa kasar Vietnam ba tare da Visa ba

Rukayya Muhammad Lawal ta kara da cewa haihuwar da Akuyar tata tayi, ya sanya ta matukar farin ciki wanda hakan yasa ta shirya gagarumin suna ta kuma gayyaci mutane daga wurare daban-daban don su zo su tayata farin ciki , sun kuma yi girke-girke kala daban-daban domin nuna farin ciki da haihuwar Akuyar Abida.

Wakilin Freedom Radiyo dake jihar Kano Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya halarci taron bikin sunan inda ya ruwaito cewa a yayin taron sunan an yiwa Akuyar Abida kasaitacciyar kwalliya ta gani ta fada tare dan Akuyan data haifa mai suna Murtala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel