Shari'ar Buhari da Atiku: Tambuwal ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun koli ta yanke

Shari'ar Buhari da Atiku: Tambuwal ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun koli ta yanke

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, ya hori shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maida komai ba komai ba sakamakon nasarar da ya samu. Ya kara da jinjinawa Alhaji Atiku Abubakar bisa ga jajircewarsa da kuma yarda da fannin shari'a na kasar nan.

"Wannan lokaci ne da yakamata shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi mulki tare da kowa don ganin habakar Najeriya," in ji shi.

A ranar Laraba ne kotun koli tayi watsi da daukaka kara da dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da jam'iyyarsa suka yi sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka kara kan shari'ar da ta jaddada nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 23 ga watan Fabrairu.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Wanne mataki Atiku zai dauka nan gaba?

"A maimakon ya goyi bayan magoya bayansa don su dinga murna, wannan lokaci ne na maida hankali wajen habaka kasar nan da ganin ta kai wani matsayi. Lokaci ne na kwo karshen kalubalen da ke addabar kasar na," in ji shi.

Ya jaddada cewa, matsayar Atiku ta taka rawar ganiwajen cigaban damokaradiyyar kasar nan. "Ina shawartar 'yan jam'iyyarmu da kada su ja da baya. Hukuncin kotun koli shine karshe. Siyasa dama ta gaji haka, ko ayi nasara ne ko kuma akasin haka," ya kara da cewa.

"Tunda dan takararmu ya zabi bin hanyar shari'a, hakan kuwa na nuna cewa bashi da son kanshi, hargitsi ko hayaniya. Dama mulki na Ubangiji ne." in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel