Tashin hankali: An kama wani mutumi da yake cin naman mutame danye

Tashin hankali: An kama wani mutumi da yake cin naman mutame danye

An kama wani mutumi a yankin arewacin kasar Rasha, inda ake tuhumarsa da laifin cin naman mutane bayan an gano wasu matattun mutane da aka cinye wasu sassa na jikinsu, tare da sauran sassan jikin wasu karnuka da wasu sauran dabbobi da suma aka cinye

Mutumin mai shekaru 51 ana zargin shi da yaudarar mutane uku ta hanyar jawo su a jikinshi sannan ya basu barasa suka sha suka bugu shi kuma sai ya kashe su tare da daddatsa naman jikinsu ya kuma fara cin wasu sassa na su.

Tuni dai masu bincike a kasar Rasha suka fara gabatar da bincike akan mutumin, sannan sun wallafa wani bidiyo da suka dauka a shafin yanar gizo, yanayin yadda wajen ya nuna ya bayyana cewa an dauki bidiyon a daidai wajen da yake cin naman mutanen.

Masana sun sanar da cewa mutumin lafiyar shi kalau, kuma kwakwalwar shi ba ta da wani matsala, sai dai kuma an gano cewa an taba kai kukan shi akan wani laifi da ya aikata, amma sai hukumar 'yan sanda ta kasar Rasha tayi kunnen uwar shegu da lamarin ba tare da ta adana rahoton ba.

KU KARANTA: Hajiya Badiyya Inuwa ta bude sabon asibiti kyauta ga masu cutar sikila a Kaduna

Bincike ya bayyana cewa an kashe wadannan mutane daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2017, sai dai kuma hukumar tsaron kasar ta bayyana cewa an dauki lokaci kafin a gano mutanen.

Yanzu haka dai biyu daga cikin mutanen an kasa gano 'yan uwansu.

Wannan mutumi dai yana haya ne a gidan wani mutumi da ya kashe, inda daga baya ya bayyana cewa yayi tafiya zuwa wani gari neman aikin yi. Ya bayyanawa iyayen shi cewa mutumin yayi tafiya sannan ya amince cewa ya zauna a gidan shi domin ya kula mishi dashi kafin ya dawo daga aikin da ya tafi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel