Mutumin da ya tsula fitsari a gaban Alkali ya samu belin N50,000

Mutumin da ya tsula fitsari a gaban Alkali ya samu belin N50,000

Alkalin wata kotun majistri dake zamanta a garin Osogbo, babban birnin jahar Osun ya sauke fushinsa a kan wani matashi dan shekara 35, Ibrahim Saheed da ake tuhumarsa da laifin sata, bayan ya shafa ma idanunsa yaji ya tsula fitsari a cikin kotu.

Jaridar Punch ta ruwaito hankalin Saheed ya tashi ne bayan an karanto masa tarin laifukan da ake tuhumarsa a gaban kotun da suka danganci sata, inda nan take ya shiga daga murya yana ihu, hakan tasa alkalin ya bada umarnin garkameshi a kurkukun Ilesha.

KU KARANTA: Ba sani ba sabo: Jami’an EFCC sun yi dirar mikiya akan manyan jami’an hukumar zabe INEC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Saheed ya tsula ma kotu fitsari ne a zaman kotun na ranar Juma’ar da ta gabata, amma a yayin zaman kotun na ranar Talata, 29 ga watan Oktoba ya shiga taitayinsa, inda ya natsu har aka kammala zaman.

Da yake gabatar da jawabi a gaban kotu, dansanda mai shigar da kara, Elisha Olusegun ya bayyana cewa Saheed ya aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Oktoban 2019 da misalin karfe 2.10 na dare a wani gida dake titin Kinikun, a unguwar Afrika.

Dansandan yace Saheed ya fasa silip din dakin wani Abdulsalam Tajudeen da nufin sata, inda yace hakan ya saba ma sashi na 411 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Osun na shekarar 2003, sai dai bayan sauraron tuhumar da ake masa, Saheed ya nemi kotu ta bashi daman daukan lauya da zai kareshi.

Daga karshe Alkalin korun, Opeyemi Badmus ya bada belin Saheed a kan kudi N50,000 tare da mutum 1 da zai tsaya masa a kan N50,000, sa’annan ya dage karar zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel