Wanda ya mutu ya mutu, dan haka ba dole ne sai na halarci jana'izar mahaifiyata ba - Nnamdi Kanu

Wanda ya mutu ya mutu, dan haka ba dole ne sai na halarci jana'izar mahaifiyata ba - Nnamdi Kanu

- Nnamdi Kanu ya bayyana hukuncin da ya dauka dangane da halartar jana'izar mahaifiyarsa

- Ya bayyana cewa ba zai taba zuwa Najeriya ba matukar hakan zai sanya mutanensu cikin matsala

- Haka kuma ya kara da cewa bai sanya kowanne sarki ya roka masa gwamnati ta kyaleshi ya shigo Najeriya ba

Shugaban 'yan gwagwarmayar kafa yankin Biafra, Nnamdi Kanu ya bayyana hukuncin da ya yanke dangane da shigowar shi Najeriya domin halartar jana'izar mahaifiyar shi.

Idan ba a manta ba mahaifiyar Kanu ta mutu a cikin watan Agustan da ya gabata amma kuma an sanar da mutuwar ta ne kwanan nan.

Nnamdi Kanu dai ya dora alhakin mutuwar mahaifiyarsa akan gwamnatin Najeriya, inda ya bayyana cewa hukumar sojin Najeriya ce ta ci zarafinta inda har hakan yayi sanadiyar mutuwar ta.

KU KARANTA: Innalillahi: Wani mugun likita ya shafawa yara sama da 900 cutar HIV bayan yayi amfani da allura guda daya a kansu

Ga dai abinda Nnamdi Kanu ya ce a wata hira da yayi da wakilin Muryar Amurya:

VOA: Kwanan nan wasu sarakuna sun bukaci gwamnati da ta kyaleka ka shigo Najeriya domin halartar jana'izar mahaifiyar ka, me zaka ce game da wannan?

Kanu: Mahaifiyata ta mutu ne sanadiyar cin zarafin ta da gwamnatin Najeriya tayi, dan haka bana bukatar kowa ya rokar mini gwamnati domin na shigo na binne mahaifiyata. Ba wai na damu da sai na zo bane idan har hakan zai yi sanadiyyar bacewa da mutuwar wasu daga cikin 'yan uwanmu. Ba zanyi duk wani abu da zai kawo matsala ga mutanen mu ba kawai akan wata jana'iza, ko ina Najeriya ko bana nan dole za'a binne mahaifiyata.

VOA: Wasu daga cikin masu kalubalantar ka sunce kana so a raba Najeriya ne kuma hakan ya sabawa doka irin ta Najeriya, me zaka ce game da haka?

Kanu: Tambayar a nan ita ce wanene ya kirkiri Najeriya? Najeriya ba ita ce ta kirkiri kanta ba, kasar Birtaniya ce ta kirkiri Najeriya. Da babu wani abu da ake kira da Najeriya kafin kasar Birtaniya ta zo. Abin da muke so shine, Najeriya ta koma kamar da a lokacin da turawan mulkin mallaka suka shigo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel