Bayan daukar lokaci muna soyayya na gano cewa budurwa ta tantiriyar 'yar iska ce ta zubar da cikin shege har sau biyu - Saurayi ya tona asiri

Bayan daukar lokaci muna soyayya na gano cewa budurwa ta tantiriyar 'yar iska ce ta zubar da cikin shege har sau biyu - Saurayi ya tona asiri

- Bayan mun shafe watanni muna soyayya da budurwata a karshe ta bayyana mini cewa da ita tantiriyar 'yar iska ce

- Saurayin ya bayyana cewa budurwar ta fada masa abinda ya faru da ita a bayan ne ba tare da ya tambayeta ba

- Ya ce yanzu haka shi kan shi ya daure bai san mene yake yi masa dadi ba, hakan yasa yake neman shawarar mutane

Wani saurayi dan Najeriya budurwar shi ta sanya shi cikin wani hali bayan ta bayyana mishi cewa ita tantiriyar 'yar iska ce.

Ga dai abinda saurayin ya wallafa a shafukan sada zumunta na yanar gizo:

"Na hadu da budurwa ta kwanannan a makaranta, ita tana yin digiri na farko ne ni kuma ina yin digiri na biyu.

"Mace ce mai matukar kyau. Mun shafe watanni muna soyayya tana da matukar mutunci, tana da kyakkyawar zuciya ba ta da mugun hali, har abubuwa take saya mini duk kuwa da cewa ni ba talaka bane, za ta zo gidana ta share mini ta gyara ko ina da ina.

"Haka kuma ta sanar dani game da tsohon saurayinta, tana son shi kuma tana taimaka mishi da kudi saboda dalibi ne kuma bashi da kudi.

"Soyayya ta da ita na tafiya babu wata matsala, sai kawai cikin daren nan ta yanke hukuncin bayyana mini abubuwan da tayi a baya bata tare dana tambayeta ba. Ta ce ina da matukar muhimmanci a gareta saboda haka ya kamata na san gaskiyar ko ita wacece.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Fulani ne za su shiga halin ni 'yasu idan Najeriya ta rabu gida biyu - Tsohon gwamnan Anambra

"Ta fara da bayyana mini cewa ta zubar da cikin tsohon saurayinta har sau biyu, ta cigaba da cewa ta yi lalata da maza da yawa saboda ta samu kudin da zata taimakawa saurayinta.

"Yanzu haka na rasa mai ke yi mini dadi kuma kaina ya daure. Ta ce mini nayi hakuri saboda ban dace da ita ba.

"Ban san yadda zanyi da wannan lamari ba saboda ta fada mini gaskiyar abinda ya faru da ita a baya ba tare dana tambayeta ba, kuma ta bayyana mini duka wannan saboda haduwar dana yi da ita."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel