Osinbajo ya bayyana abinda Najeriya ke bukata kafin ta samu cigaba

Osinbajo ya bayyana abinda Najeriya ke bukata kafin ta samu cigaba

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya akwai bukatar jagoranci nagari a Najeriya.

Ya ce domin samun damar cimma hakan, gwamnatin tarayya ta kafa hukumomi da cibiyoyi daban-daban.

Osibajo, wanda ya samu wakilcin Maryam Uwais, mai taimaka wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da shawara a kan harkokin walwalar jama'a, ya bayyana hakan ne yayin wani taro na kasa da kasa da halarta ranar Talata a Abuja.

A cewarsa. "mu na bukatar jagoranci nagari a Najeriya. Akwai bukatar mu kaurace wa rashin adalci, cin hanci da rasha wa da kuma aikata duk wani abu da kan iya zama cin zarafin mutane, maza ko mata.

Kwamishinan hukumar karbar korafin jama'a, Mista Chille Igbawua, ya ce an shirya taron ne domin tattauna wa a kan hanyoyin da za a inganta mulki da kwazon jagorori.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel