Mamakon ruwan sama ya yi ajalin wata budurwa a cikin keke Napep a Kaduna

Mamakon ruwan sama ya yi ajalin wata budurwa a cikin keke Napep a Kaduna

Hankula sun tashi a unguwar Hayin Malam Bello dake cikin yankin Rigasa na karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna yayin da mamakon ruwan sama ya yi awon gaba da wata babur din keke Napep har ya yi sanadiyyar mutuwar wata budurwa.

Wannan lamari ya faru ne da yammacin Lahadi, 27 ga watan Oktoba da misalin karfe 6, a lokacin da aka tsaka da ruwan sama kamar da bakin kwarya, inda ruwan ya mamaye gadar shiga Hayin Malam Bello.

KU KARANTA: A karon farko: Najeriya ta fara dinka ma kafatanin jami’an tsaronta khaki a cikin gida

A wannan yanayi ne direban Keke Napep dauke da mutane 3 a ciki, mata 2, namiji 1, ya yi kokarin hayewa gadar duk da ruwan daya malale kan gadar, a dalilin haka ruwan ya korasu zuwa cikin rafi, sai dai direban da fasinjan namijin sun sha da kyar.

Yayin da kyar jama’a suka ceto guda daga cikin matan, inda ruwan ya yi awon gaba da yar uwarta, duk kokarin da jama’a suka yi na cetota ya ci tura sakamakon karfin ruwan, wanda hakan yasa dole kowa ya hakura ya dawo.

Legit.ng ta ruwaito wani mai shago dake kusa da gadar Hayin Malam Bello ya bayyana cewa: “Jim kadan bayan an ceto daya daga cikin matan, sai muka ji tana magana a waya tana fadin cewa Balaba na cikin ruwa, tana fada tana kuka.”

Ko da yake tun kafin yanzu, al’ummar unguwar Hayin Malam Bello sun jima suna kokawa a kan aikin da tsohuwar gwamnatin Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ta yi wajen gina wannan gadar, saboda a duk lokacin da aka yi ruwan mai karfi sai ya shanye gadar, ya kuma hana kowa wucewa saboda ya yi kasa sosai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel