Buhari ya jajanta ma iyalan Tafawa Balewa game da mutuwar uwargidarsa

Buhari ya jajanta ma iyalan Tafawa Balewa game da mutuwar uwargidarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da mutuwar uwargidar marigayi tsohon firai ministan Najeriya, Sir Abubakar Tafawa Balewa,Hajiya Jummai Abubakar da ta rasu a ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa Hajiya Jummai ce matar Tafawa Balewa kadai data rage da rai, amma a ranar Lahadi ta rasu a jahar Legas tana mai shekaru 90 a duniya.

KU KARANTA: Matar Tafawa Balewa da ta rage a duniya ta mutu

Buhari ya jajanta ma iyalan Tafawa Balewa game da mutuwar uwargidarsa
Jummai
Asali: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a sakon ta’aziyyarsa daya fitar ta bakin hadiminsa a kan hula da jama’a, Malam Garba Shehu, shugaba Buhari ya bayyana cewa; “Na kadu matuka game da samun labarin rasuwar Hajiya Jummai Tafawa Balewa.

“Mutuwarta ta sa Najeriya ta yi rashin jigo a siyasar Najeriya wanda ta taimaka matuka wajen ciyar da iyalan Tafawa Balewa gaba, tare da dukkanin akidun maigidan nata. Don haka ina mika ta’aziya ga iyalan Tafawa Balewa da kuma jama’an Bauchi gaba daya, Allah Ya jikanta.” Inji shi.

Haka zalika Buhari ya umarci sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha da ya yi amfani da guda daga cikin jiragen shugaban kasa domin a dauki gawar Hajiya Jummai daga Legas zuwa jahar Bauchi domin a yi mata jana’aiza.

Ana sa ran a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba ne za’a gudanar da jana’izar Jummai a jahar Bauchi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel