Mudassir and Brothers: Dan kasuwa zai gina kamfanin atamfa na $50m a Kano

Mudassir and Brothers: Dan kasuwa zai gina kamfanin atamfa na $50m a Kano

Alhaji Mudassir Idris Abubakar, wani dan kasuwa da ya mallaki katafaren shagon sayar da sutura a Kano, Mudassir & Brothers, ya ce ya fara shirye-shiryen da zasu kai shi ga gina kamfanin atamfa na dalar Amurka miliyan biyar ($5m).

Dan kasuwar ya ce zai bude kamfanin ne domin bunkasa tattalin arzikin jihar Kano da kasa baki daya ta hanyar samar da guraben aiyuka ga matasa.

Da yake gana wa da manema labarai a ofishinsa ranar Asabar, Alhaji Mudassir Idris Abubakar, ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar Kano ta bashi filin da zai gina kamfanin tare da bayyana cewa yana cigaba da sauran shirye-shiryen fara aikin gina kamfanin.

DUBA WANNAN: Buhari zai tafi Saudiyya tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 da wasu sauran hadimai

"Ina son mika godiya ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa kokarinsa na son ganin jihar Kano ta dawo matsayinta na jihar da ta yi suna wajen kera atamfa da kuma ba ni kyautar fili domin gina kamfanin," a cewarsa.

Mudassir ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta bashi fili mai girman hekta 22.5 domin nuna goyon bayanta ga niyyarsa ta son gina kamfanin.

Kazalika, ya bayyana cewa kamfanin zai samar da guraben aiyuka 10,000 tare da bayyana cewa yanzu haka yana da ma'aikata a kalla 500 da ke aiki a karkashinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: