Rayuwa: Tsohon gwamnan PDP a jihar arewa ya talauce bayan an kwace katafaren gidansa a Abuja

Rayuwa: Tsohon gwamnan PDP a jihar arewa ya talauce bayan an kwace katafaren gidansa a Abuja

Hausawa na cewa duniya juyi - juyi, tamkar rawar 'yammata, na gaba ya koma baya. Watau, idan yau kai ne, gobe ba kai ne ba. Irin wannan juyin rayuwa ne jaridar Thisday ta wallafa cewa ya faru da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda.

Thisday ta rawaito ce tsohon gwamna Yugudu, wanda ya fara cin mulki a karkashin inuwar jam'iyyar ANPP kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP, ya shiga sahun tsofin masu mulki da za a iya cewa sun talauce duk da irin daula da arziki suka tara lokacin da suke kan mulki.

Jaridar ta bayyana cewa duk irin makudan kudi da tarin kadarorin da tsohon gwamnan ya mallaka lokacin da yake kan kujerar mulki basu hana karayar arziki ta fada masa ba sakamakon bashi da ya yi masa katutu.

Tun bayan kammala wa'adinsa na biyu a shekarar 2015, Yuguda ke 'fadi tashi' daga wannan inuwa zuwa waccan domin guje wa tsegumi irin na yan jarida da kuma ganin hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) bata shiga farautarsa ba.

A cewar rahoton Thisday, wata majiya mai kusanci da tsohon gwamnan ta sanar da ita cewa ya fara sayar da kadarorinsa, musamman filaye, gidaje da gonaki.

DUBA WANNAN: Majalisa ta aika wa tsohon gwamnan APC sammaci, ta lissafa manyan zunubansa 5

Duk da tsohon gwamnan ya yi nasarar tsere wa binciken hukumar EFCC, Thisday ta ce bai iya samun nasarar tsere wa tafka asarar kadarorin da ya mallaka ba lokacin da yake sharafinsa a gwamnati.

Alal misali, tsohon gwamna Yugudu ya mallaki sayi wani katafaren gida a unguwar Asokoro da ke Abuja a kan farashin naira biliyan uku (N3bn), amma yanzu haka bashin da ake binsa ya yi sanadiyar raba shi da gidan.

A cewar majiyar Thisday, yanzu haka wannan babbar kadarar da tsohon gwamna Yugudu ya mallaka tana hannun wani babban kwamandan rundunar sojin sama, Mohammed Umar Gololo.

Jaridar ta ce bata da masaniya ko karin bayani a kan yanayin harkar kasuwancin da ta shiga tsakanin Yuguda da Gololo har ta kai ga an damka masa katafaren gidan amadadin bashin miliyan N400 da yake bin tsohon gwamnan.

Haka tsohon gwamnan ya cigaba da sayar da manyan kadarorinsa a Bauchi da Abuja, a cewar rahoton jaridar Thisday.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel