Cututtuka 10 da abarba ke magani a jikin dan Adam

Cututtuka 10 da abarba ke magani a jikin dan Adam

– Kayan marmari su na da matukar amfani ga jikin Dan Adam

– Daga cikin masu irin wannan amfani akwai Abarba

– Abarbara na gina jiki kuma yana maganin cututtuka da dama

Musamman ma ta fuskar kare jiki daga kamuwa da ciwon zuciya, abarba na daya daga cikin 'ya'yan itatuwa masu amfani a jikin dan adam.

Abarba na da matukar amfani a jikin dan adam a sanadiyar arzikin wasu muhimman sunadarai da ta kunsa kamar su; fibres, minerals, calcium, manganese, vitamins, Nutrient da kuma Anti Oxidant.

Wadannan sinadarai da abarba ta kunsa na taka muhimmiyar rawar gani wajen amfani ga rayuwar dan adam, sannan takan kare jiki daga cututtuka.

Ga jerin cututtuka da kuma illoli da dama da abarba ke magancewa a jikin dan Adam:

1. Cutar Arthritis: Abarba na maganin cutar nan ta atiraitis mai sanya rikewar gabbai da jijiyoyi inda su ke kumbura har su hana mutum sakat.

2. Cutar Daji (Cancer): Abarba na maganin cutar ‘kansa’ mai lahanta kwayoyin garkuwa saboda sinadarin da ta kunsa na vitamin A da C da sauran su.

3. Sanyi da mura: Yawaita shan abarba na bayar da kariya daga cututtuka na mura da sanyi domin kuwa tana kunshe da wasu sinadarai da ke kashe majina.

4. Karfin hakori: Kadan daga aikin Abarba akwai kara karfin jijiyoyin hakori ta kuma kara lafiyar dasashi da kare hakora daga cututtuka. Tana kuma kara lafiya da gyara suma watau gashi na jikin mutum.

5. Karfin gani: Haka kuma abarba na kara kaifin idanu don haka mai shan abarba zai dade da idanun sa garau ko ya tsufa.

6. Hawan jini: Abarba na kare cutar hawan jini saboda sindarin Pottasium da take dauke da shi mai amfani wajen yawo da jini a jikin mutum.

7. Abarba na hana tsufa: Abarba ta tsaya ga gyaran idanu kadai ba yayin da tsufa ya cimma mutum domin kuwa tana kare mutum daga cutar dimuwa, mantau da sauran cututtuka na tsufa.

8. Tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage daskararren maiko wato cholesterol a jiki.

KARANTA KUMA: Sirrika 10 na ganyen gwaiba wajen bunkasa lafiyar bil Adama

9. Tana saukaka yawan laulayin ciki, da yawan amai da tashin zuciya. Tana maganin tsutsar ciki da saukaka fitar bahaya.

10. Abarba tana inganta garkuwar jiki, lafiya da kare shi daga cututtuka.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng