Faisal Maina: Dan Abdulrashid Maina da ya zare bindiga a lokacin da za a kama mahaifinsa (Hotuna)
An gurfanar da Faisal Maina, dan tsohon shugaban hukumar fanshon ma'aikata, Abdulrasheed Maina, a gaban kotu.
A ranar Juma'a ne wata babbar korun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin a tsare Abdulrasheed Maina a gidan yari bayan hukumar EFCC ta gurfanar da shi.
Maina ya gurfana a gaban kotun ne tare da dan sa mai shekaru 20, Faisal, wanda ya zare a lokacin da jami'an tsaro suka yi yunkurin kama mahaifinsa bayan ya shigo Najeriya kimanin sati biyu da suka wuce.
DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kama dan majalisa a APC daga arewa da hannu dumu-dumu a garkuwa da mutane
Alkalin kotun, Jastis Okon Abang, ya bayar da umarnin tsare Maina ne bisa bukatar hukumar EFCC bayan ya musanta dukkan tuhuma 12 da ake yi masa a gaban kotun.
Alkalin kotun ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba domin duba takardar bukatar neman beli da Maina ya gabatar ta hannun lauyansa.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Hukumar EFCC ta dade tana farautar Maina domin gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da almundahanar makudan kudaden da ya wawyre lokacin da yake jagorantar hukumar gyaran harkar fansho.
Maina ya sulale ya bar Najeriya a karshen mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, bayan an fara bincike a kansa.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa an mayar da Maina bakin aiki a gwamnatin shugaba Buhari duk da laifukan da ake zarginsa da aikata wa da kuma kasancewar ya gudu zuwa ketare. Lamarin ya jawo cece-kuce kafin daga bisani maganar ta mutu ba tare da an fahimci gaskiyar zancen ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng