Hotunan katafaren filin wasan kwallon kafa na Kahutu da Rarara ya gina

Hotunan katafaren filin wasan kwallon kafa na Kahutu da Rarara ya gina

Rahoton da muka samu daga labarai24.com ya tabbatar da cewa fitaccen mawakin siyasan nan Adamu Kahutu Rarara ya gina katafaren filin wasan kwallon kafa a garin Kahutu da ke jihar Katsina a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Hakan na nuna cewa jihar Katsina ta samu karuwa a fanin wasanni duba da cewa akwai filin wasan Katsina United da ke birnin Katsina a jihar.

An sanyawa wannan babban filin wasan 'Rarara Stadium' don karrama fitaccen mawakin da ya koma gida jiharsa don ya bayar da na sa irin gudunmawar wurin inganta rayuwar matasa ta hanyar wasanni da motsa jiki.

Tun kafin gina wannan filin wasan, fitaccen mawakin yana da kungiyar horas da 'yan kwallo mai suna Rarara Academy da ya rikede ya zama babban kungiyar kwallon kafa.

Kungiyar ta Rarara Academy tana daga cikin kungiyoyin da ke buga kwallo a gasa mai daraja ta biyu a kasar nan wato Nigerina National League.

DUBA WANNAN: Ban iya magana da harshen hausa sosai ba - Zahra Buhari

Kungiyar da Rarar Academy ta taka rawar gani a gasar sharar fage da a kayi a jihar Kano inda har ta kai matakin kusa da na karshe har na neman na uku suka fafata da kungiyar Jigawa Golden Stars inda suka yi rashin nasara.

Ga hotunan a kasa:

Hotunan katafaren filin wasan kwallon kafa na Kahutu da Rarara ya gina
Hotunan katafaren filin wasan kwallon kafa na Kahutu da Rarara ya gina
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel