Lafiya Jari: Sirrin ruman a jikin dan Adam

Lafiya Jari: Sirrin ruman a jikin dan Adam

Shi dai itace ruman a turance ana kiran sa Pomegranate, kuma ya samo wannan suna ne daga sunan sa larabci wato Rumman, inda Allah madaukakin sarki ya ambace sa a wurare daban-daban a cikin ayoyin sa na Al-Qur'ani mai girma.

Ruman A sakamakon haka ne, wannan dan itace ya kasance daya daga cikin 'ya'yan itace masu matuƙar muhimmacin a duniya, domin kuwa Allah ya ambace shi a cikin aya guda tare da itacen zaitun, inda ya ƙunshi tarin sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam.

Wannan dan itace ya ƙunshi sunadarai da suka hadar da; Fiber, Protein, vitamin C, vitamin K, Folate da kuma Potassium.

KARANTA KUMA: Lafiya Jari: Amfanin dariya 6 ga lafiyar dan Adam

Legit.ng ta kawo muku jerin cututtakan da dan itace ruman ke magancewa a sakamakon arzikin wannan sunadarai da ya ƙunsa:

1. Ciwon Zuciya.

2. Ciwon daji (musamman na mama, maraina da kuma mahaifa).

3. Rage teɓa da nauyin jiki.

4. Ciwon Sukari.

5. Hawan jini.

6. Cututtukan rashin ƙarfin mazakuta.

7. Kumburin jiki da ciwon gaɓɓai.

8. Cutar hauka da mantau.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng