Lafiya Jari: Amfanin dariya 6 ga lafiyar dan Adam
Mutane da dama kan yi dariya ne a yayin da suke cikin nishadi ko walwala. Wani abun al'ajabi na dariya shine ba ta da yare ko kabila domin kuwa kowa na yinta, sai dai da yawan masu yin dariya ba su da masaniyar amfani da take dashi ta fuskar kiwon lafiyar dan Adam.
A yau dai bankade-bankade na jaridar Legit.ng ya binciko muhimmancin yin dariya ga lafiyar dan Adam wadanda suka hadar da:
1. Yin dariya yana sanya inganta lafiyar fuskar mutum ta kara kyawu, inda wasu ke mata kirarin maida tsohuwa yarinya.
2. Wani bincike da aka gudanar a jami'ar Michigan ta Kasar Amurka ya bayyana cewa, yin dariya na sakwanni 20 kacal yana inganta lafiyar hunhu na dan Adam ta hanyar yin numfashi mai inganci.
3. Dariya tana kara garkuwar jiki wajen yakar cututtuka, sakamakon wani bincike da aka gudanar a cibiyar lafiya ta jami'ar Loma dake birnin Carlifonia na kasar Amurka, wanda wani likita Dakta Lee Berk ya gudanar a shekarar 1989.
KARANTA KUMA:
4. Binciken shekarar 1995 da wani likita na kasar Indiya Dakta Madan Kataria ya gudanar a birnin Mumbai ya bayyana cewa, yin dariya yana sassauta cututtukan zuciya, cutar hawan jini da ciwon sukari.
5. Yin dariya yana sanya mutum ya rage teba da kuma nauyin jiki.
6. Bincike ya bayyana cewa, yin dariya kafin kwanciyar bacci tana sanya bacci mai tsayi da kuma dadi.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng