Safiyya Ahmad, ta lashe gasar Hikayata na bana
- Safiyayya Ahmad ce marubuciyar da ta lashe gasar rubutun Hausa na mata da BBC ta shirya na wannan shekarar
- Asalinta 'yar karamar hukumar Zaria ce ta jihar Kaduna a arewacin Najeriya
- Labarin 'Maraici' yana magana ne akan Karima wacce ta tashi a gidan marayu amma wata mata ta dau nauyinta
Safiyya Ahmad ce marubuciyar da ta lashe gasar rubutun hausa na mata na BBC a wannan shekarar.
Safiyya Ahmad mai shekaru 23 haifaffiyar karamar hukumar Zaria ce ta jihar Kaduna arewacin Najeriya. Ta lashe gasar ne da rubutunta mai suna 'Maraici'.
Maraici dai gajeran labari ne akan wata yarinya mai suna Karima wacce aka watangarar tun tana jinjira. Ta girma a gidan marayu inda Hajiya Babba ta dauketa. Ta sanyata makarantar firamare da sakandire inda daga baya ta aurar da ita. Amma sai auren ya mutu kuma Hajiya Babba ta juya mata baya.
KU KARANTA: Majalisar tarayya ta dau zafi, ta juyawa Minista Sadiya Umar Farouq baya
A shekarar da ta gabat ne Safiyya tayi yunkurin cika burinta na zama marubuciya. Bayan jin labarin gasar rubuta ta BBC ta mata, ta zauna ta tsara labarin maraici bayan kalubalen da ta fuskanta daga mutuwar mahaifinta da kuma labaran da ta samu daga mahaifiyarta.
Wannan gasa dai na shekararta ta hudu da farawa. An kirkirota ne kuma don bawa marubuta mata damar bayyana labaransu.
Safiyya Ahmad ta yi makarantar Sunnatullah da kuma Suntal inda ta samu ilimin firamare da na sakandire. A halin yanzu tana rayuwa da mijnta tare da 'yarta.
Bayan da Safiyya ta bar karatusakamakon mutuwar mahaifinta, a halin yanzu tana karatu a makarantar kimiyyar lafiya ta Jama'atu dake Zaria.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng