Sarakuna 3 ne kadai ba su da hannu a matsalar tsaron jahar Zamfara

Sarakuna 3 ne kadai ba su da hannu a matsalar tsaron jahar Zamfara

Kwamitin bincike a kan matsalar tsaro a jahar Zamfara da gwamnan jahar, Bello Matawalle ya kafa domin bankado musabbabin rikicin tare da duk masu sa hannu cikin rikicin ta mika rahoton bincikenta, inji rahoton jaridar Aminiya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan kwamiti yana karkashin jagorancin tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad D Abubakar, kuma kwamitin ta bayyana cewa sarakuna guda 3 ne kacal basu da hannu a cikin matsalar tsaro a jahar.

KU KARANTA: Hukumar kwastam ta cika hannu da buhu 149 na haramtacciyar shinkafa a Kaduna

Kwamitin ta nemi gwamnatin jahar Zamfara ta sauke sarakuna guda biyar daga sarautarsu, sauran wadanda kwamitin ta bada shawarar a sallamesu sun hada da uwayen kasa 33, da kuma hakimai da dama.

Shugaban kwamitin, Muhammad Abubakar ya ce kwamitin nasa ya mika bukatar warware rawunan sarakunan ne bayan da ya same su da hannu dumu-dumu cikin matsalar tsaron da ya addabi jihar shekara da shekaru.

Kwamitin ta kara da cewa ta samu karin bayanai daga cikin wasu tubabbun ’yan bindiga da ta tattauna da su a yayin binciken nata inda suka shaida musu cewa wadansu sarakunan na da hannu wurin tilasta musu daukar makamai.

Kwamitin ya bukaci gwamnati ta yi wa tsarin masarautun jihar garambawul, yana mai cewa sarakunan jihar sun zama tamkar maroka a hannun al’ummomin da suke mulki a jihar.

Haka zalika kwamitin ya bukaci a karrama wasu sarakuna ta hanyar basu lambar yabo saboda rawar da suka taka wajen tabbatar da doka da adalci a masaurutunsu. Kuma akwai ’yan sanda da sojoji da ma’aikatan gwamnati da kwamitin ya bukaci a kore su daga aiki, baya ga wadanda ya ce a yi musu karin girma saboda kokarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel