Ciwon hanta da sauran illoli 7 da shan ruwan sanyi ke haifar wa ga lafiyar dan Adam
Babu shakka ruwan sanyi wani sinadari ne mai matukar sanyaya zuciya musamman ma a irin wannan lokacin da ake zabga tsabagen zafi. Wannan ne ma yasa yawancin mutane idan sun fita sun sha rana basu da wani buri da ya wuce su samu ruwan sanyin su kwankwada.
Haka ma dai zamani ya saukaka wa jama'a hanyoyin samun ruwan sanyin inda yanzu akwai na'urorin sanyaya ruwa da dama a gidajen mutane.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin illolin da ruwan sanyin ke yi a jikin dan adam
1. TSAYAR DA BUGUN ZUCIYA
Bugun zuciya shike daidaita dumin jiki ya kuma daidaita numfashi inda ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. Ko kunsan yawancin yan fim na kasar indiya da yan kwallo da 'yan dambe da kokawa, tsayawar bugun zuciya ke ajalinsu kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi yayin da suke aiki ne yake jawo musu.
2. LALATA TSARIN KAYAN CIKI
Shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji guri daya sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri hakan kan jawo matsalar hanji ulcer kenan ko kuma tashin zuciya. Yawancin masu shan ruwan sanyi suna yawan zubda yawu ko tashin zuciya ko saurin kullewar ciki.
3. KASALA DA LALACI
Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji dadi amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon cewa yayin da ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai na'urorin jikin sunyi kokarinsu na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin, hakan yana sa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi. Ko kun lura duk yayin da kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk sanyin ya ratsa kaman farkon zazzabi a hankali kuma sai kuji ya daina?
4. CIWON MAKOSHI DA DAKUSHEWAR MURYA
Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro har sukai ga basa amfaninsu mai kyau. Idan mai yawan shan ruwan sanyi ya kai shekaru arba'in sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya ko muryar ta fashe kwatankwacin mashayin taba.
KARANTA KUMA: An nada Sa'a Ibrahim sabuwar shugaba ta kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya
5. CIWON HANTA DA KODA
Hanta da Koda suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu don haka yayin da bawa ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara raguwa inda haka ke jefa mutum cikin matsala.
6. BUSAR DA RUWAN JIKI
Akwai na'urori a jikin dan Adam da aikinsu shine sadar da ruwa ko ina a jikin mutum ta yanda ko ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi. To wadannan na'urorin sukan yi sanyi sakamakon ruwan sanyi sai su zama basu da wani karfi.
7. MATSALAR MA'AURATA
Wannan abune tabbatacce harga likitocin zamani cewa shan ruwan sanyi yana raunata mazakutar namiji a yayin da kuma yake busar da mace in mahaifarta nada rauni da hakan yake iya hana haihuwa. Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin inzali ko kuma ya rage masa kuzari. Yana dauke ni'imar jiki su zamo basa gamsuwa da juna.
8. BASIR DA CIWON KAI NA KWIBI (MIGRAINE)
Shan ruwan sanyi yana tattare hanji hakan yana kawo wa lafiyar mutum cikas ta yadda zai kasa bayan gida face ya hadu da basir. Sannan yana kawo ciwon barin kai wanda ake cewa migraine. Shi kuma migraine yana kashe jijiyoyin ido a daina gani sosai in yayi nisa har hauka yana sawa.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng