Lafiyar zuciya da amfani 2 da citta ke yi a jikin dan Adam

Lafiyar zuciya da amfani 2 da citta ke yi a jikin dan Adam

Binciken masana nazari a kan kiwon lafiya ya bayyana amfanin citta a jikin dan Adam.

Tun tsawon shekaru sama da 4, 700, mutanen kasar Sin da Indiya ke amfani da citta wajen magance cututtuka daban-daban.

Citta tayi kaurin suna wajen amfani da ita cikin girki don sanya kanshi da dandano ga abinci kuma amfanin ta wajen kiwon lafiya ba zai musaltu ba.

Ga yadda hanyoyi uku na amfani da citta ke tseratar da rayuwar dan Adam

1. Bugun zuciya da sauran cututtukan masu nasaba da zuciya

Bincike ya nuna cewa idan aka yi amfani da citta tare da wasu kayan abinci irinsu tafarnuwa da albasa, su na hana daskarewar jini a jikin dan Adam wanda suke bunkasa karfin jini da zai rinka zagayawa a cikin tashoshin jini wanda hakan zai hana bugun zuciya da bayar da kariya daga sauran cututtukan zuciya.

2. Rashin cin abinci da tashin zuciya

Amfani da citta bai tsaya wajen warkar da ciwon ciki kadai ba, don tun shekaru dubunnai da su gabata a ke amfani da ita wajen warkar da matsalar rashin cin abinci da tashin zuciya.

KARANTA KUMA: An nada Sa'a Ibrahim sabuwar shugaba ta kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya

3. Rashin narkewa da tacewar amfanin abinci a cikin ciki

Citta tana inganta narkewar abinci da wuri a cikin cikin dan Adam domin wasu nau'ukan abinci suna jimawa kafin su narke. Bincike ya nuna cewa amfani da citta yana habaka saurin narkewar abinci don idan abinci ya jima a cikin mutum bai narke ba sai ya lalace wanda hakan na iya gadar da matsala ga lafiyar dan Adam.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng