Kotun Kano ta tsare wasu maza 2 da mace 1 kan laifin kwartanci

Kotun Kano ta tsare wasu maza 2 da mace 1 kan laifin kwartanci

Wani alkalin kotun Majistare, Muhammad Jibril, ya yankewa Sa’idu mai shekara 49, Adam mai shekara 45 da Nazir mai shekara 40 hukunci bayan sun amsa laifin wasu tuhume-tuhume biyu da ake masu na hada kai wajen aikata laifi da kuma kwartanci.

Jibril, wanda ya ba masu laifin damar biyan tarar N5,000 kowannensu, ya bayyana cewa suna da damar daukaka kara akan hukuncin cikin kwanaki 30.

Da farko, dan sanda mai kara, Inspekta Pogu Lale ya fada ma kotun cewa wadanda ake karan sun aikata laifin ne a kasuwar Rimi Kano a ranar 3 ga watan Oktoba, da misalin 10:15 na dare.

Ya bayyana cewa Adam, mai gadi wanda ke zama a yankin Hotoro a Kano, ya bude kofar kasuwar ga Sa’idu da kuma Nazir.

KU KARANTA KUMA: Wani dan bautar kasa ya yiwa wani yaro duka har lahira a Kano

Lale ya bayyana cewa Sa’idu da Nazir na zuwa kwartanci a kasuwar bayan sun san cewa basu da aure.

Yace laifin ya kara da sashi na 85, 387 da 388 na doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel