Allah mai iko: An haifi wani jariri babu fuska a kasar Portugal

Allah mai iko: An haifi wani jariri babu fuska a kasar Portugal

- An kori wani babban likita a kasar Portugal sanadiyyar sakacin da ya nuna a wajen aikin sa

- An kori likitan ne bayan an haifi wani yaro babu fuska a tare da shi

- Yaron dai ya zo duniya ne babu ido, hanci da sauran siffofi na fuskar mutum

An kori wani babban likitan mata a kasar Portugal bayan wata mata mai ciki ta haifi jariri babu ido, hanci da kuma wasu bangarori na kokon kansa.

Iyayen wannan jariri dai mai suna Rodrigo ba san da cewa dan nasu yana da wannan nakasu ba har sai bayan da suka haife shi a farkon wannan watan na Oktoba da muke ciki.

Hukumomin majalisar likitoci ta kasar sun yanke shawarar dakatar da Dakta Artur Carvalho a bisa zargi da yin wasa da aikinsa.

Wannan lamari dai ya jawo kace-nace a kasar ta Portugal bayan da kafafen yada labarai suka dinga baza labarin babu dare babu rana.

Har ya zuwa yanzu dai likitan da aka kora din bai ce komai dangane da wannan zargi da ake yi masa ba.

An haifi wannan jariri da aka sanyawa suna Rodrigo a ranar 7 ga watan Oktoba dinnan a wani asibiti mai suna Sao Bernardo dake garin Setubal a yankin kudancin Lisbon.

Dakta Carvalho ne dai yake kula da mahaifiyar jaririn tun daga lokacin da ta samu juna biyun yaron, iyayen jaririn sun bayyana cewa likitan bai taba nuna musu cewa akwai wata damuwa ba dangane da yaron duk kuwa da ya sha daukar hoton cikin.

KU KARANTA: Hotuna: Wata makarantar firamare da dalibai ke daukar darasi a ajin bukka, gindin bishiya kuma shine ofishin hedimasta

"Ya yi mana bayani cewa a lokuta da dama ba a ganin wasu sassa na jikin fuskar jaririn a idan aka yi hoton ciki," 'yar uwar iyayen jaririn ta shaidawa jaridar AFP.

Bayan an haifi jaririn an shaidawa iyayensa cewa ba zai rayu ba. Sai dai kuma yanzu haka sama da mako biyu kenan da haihuwar jaririn kuma har yanzu yana nan da ransa.

Kamar yadda BBC ta bayyana iyayen jaririn sun shigar da korafi akan likitan ga ofishin babban mai shigar da kara na Portugal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel