'Yan Kwankwasiyya sun yi magana kan sakon taya murna da Ganduje ya aike wa Kwankwaso

'Yan Kwankwasiyya sun yi magana kan sakon taya murna da Ganduje ya aike wa Kwankwaso

Sakon taya tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabiu Musa Kwankwaso murnar zagoyowar ranar haihuwarsa da gwamnan Kano mai ci yanzu, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya wallafa a jaridu ya janyo mahawarra tsakanin magoya bayan 'yan siyasan biyu.

A ranar Talata 22 ga watan Oktoban 2019 ne Gwamna Ganduje ya saka sakon taya murna mai daukan hankali a shafin jarida inda ya taya Dr Kwankwaso murnar cika shekaru 63 da haihuwa.

An wallafa sakon taya murnar ne kwana guda bayan magoya bayan 'yan siyasan biyu sunyi arangama a karkashin wata sabuwar gada a Madobi road a Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani dan gani kashe nin Kwankwaso, Alhaji Sanusi Surajo Kwankwaso ya ce an yi wa magoya bayan Kwankaso da yawa rauni an kuma lalata motocci fiye da 20.

DUBA WANNAN: Na yi wa 'ya'ya na biyu fyade ne don gwada kuzari na - Mahaifi

Yayin da magoya bayan Kwankwaso ke ganin sakon taya murnar dabara ce kawai don kawar da hankulan mutane kan abinda ya faru, takwarorinsu na APC suna ganin alama ce da ke nuna karamci da girmamawa ga Kwankwaso.

Alhaji Sanusi Surajo Kwankwaso ya shaidawa Daily Trust cewa sakon taya murnar ba ta da ma'ana a wurinsu don munafinci ne inda ya ce "Ta ya ya za ku kai mana hari a yau sannan gobe ku tafi shafukan jaridu kuna taya shugaban mu murna. Ya ya za kuyi tsamanin za mu amince da sakon?"

A yayin da ya ke mayar masa da martani, jigo a jam'iyyar APC, Abdulmajid Danbalki Kwamanda ya ce Ganduje ya kyauta da ya taya tsohon gwamnan murna.

Ya ce, "Ganduje ya nuna dattaku. Ya nuna wa duniya cewa yana girmama Kwankwaso. A gani na, Ganduje ya nuna cewa shi dattijo ne. Wannan sakon taya murnar ba ta da alaka da siyasa kamar yadda 'yan Kwankwasiya suke ikirari."

Kazalika, shugaban APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ya yi watsi da zargin da 'yan Kwankwasiyya suka yi ne cewa 'yan APC ne suka kai musu hari inda ya ce, "gwamnati ko APC ba su da hannu cikin abinda ya faru.

Ya ce, "Ni ban san da batun ba ma sai lokacin da 'yan jarida suka tuntube ni don jin ta ba ki na."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel