Shafaffu da mai: Diyar Goje ta samu kulawa ta musamman domin darewa mukamin kwamishina

Shafaffu da mai: Diyar Goje ta samu kulawa ta musamman domin darewa mukamin kwamishina

Majalisar dokokin jahar Gombe ta umarci diyar tsohon gwamnan jahar Gombe, Sanata Danjuma Goje ta ‘rusuna ta tafi’ a yayin da ta bayyana a gabansu domin yan majalisar su tantanceta don zama kwamishina.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito Hajiya Hussaina Danjuma Goje wanda take wakiltar karamar hukumar Akko yar shekara 35 dake da kwalin digirin digirgir ta bayyana gaban majalisar ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Yadda wani ma’aikaci ya kona ofishinsa bayan ya yi awon gaba da N1.4m

Hussaina ta bayyana ganan majalisar ne tare da wasu mutane 7 da gwamnan jahar Gombe, Inuwa Yahaya ya tura sunayensu ga majalisar, bayan ta gabatar da kanta a gaban yan majalisar, sai yan majalisu dake wakiltar Akko ta yamma da Akko ta tsakiya, Abdullahi Abubakar da Abubakar Mohammed suka nemi majalisar ta daga ma Hussaina kafa.

Dan majalisa Abdullahi da dan majalisa Abubakar sun nemi wannan alfarma daga majalisar ne sakamakon gudunmuwar da mahaifin Hussaina, Sanata Danjuma Goje yake bayarwa ga cigaban jahar Gombe.

Bayan sauraron bukatar yan majalisun, mataimakin kaakakin majalisar, Shuaibu Adamu Haruna ya amince da bukatarsu, sa’annan ya umarci Hussaina ta ‘rusuna ta tafi’ “saboda kwarewarta da kuma kimar Sanata Danjuma Goje.” Inji shi.

Sauran wadanda suka ci moriyar ‘rusuna ka tafi’ sun hada da Naomi Joel Awak daga Kaltungo, Alhaji Adamu Dishi daga Funakaye, Usman Jahun Biri daga Nafada da kuma Batari Dauda Zambuk daga Yamaltu Deba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel