Bidiyo: Cikin dalibai ya duri ruwa bayan an gano aljanar ruwa wacce ta jima tana zaune cikin dalibai da siffar mutane a wata jami'ar kasar nan
- Dalibai sun rikice a cikin makaranta bayan wata daliba ta bayyana cewa ita 'yar ruwa ce
- Hakan ya sa dalibai fitowa daga cikin dakunan su da gudu domin neman mafaka daga wannan aljana
- Lamarin dai ya biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin ita dalibar da kuma wata kawarta a cikin makarantar da daddare
A yadda wani rahoto yake ta yawo a kafafen sadarwa, wata daliba a jami'ar jihar Legas ta bayyana cewa ita 'yar ruwa ce, ma'ana aljanar ruwa.
Bayan jin labarin cewa ita 'yar ruwa ce dalibai sun fara gudun famfalaki daga cikin dakunan kwanansu suna neman mafaka.
Dalibar wacce ta bayyana cewa ita 'yar ruwa ce an bayyana sunanta da Olamide, an ruwaito cewa sun samu dan rikici da wata kawarta da suke zaune daki daya, inda Olamide ta zargi Blessing da dauke mata sarka da dan kunne, inda ta fara barazanar daukar mataki akan Blessing idan har ba ta fito mata da kayan ta ba.
KU KARANTA: Wata sabuwa: Za'a karrama zakin da ya kufce daga gidan Zoo na Kano
Wani wanda lamarin ya faru a kan idon sa ya wallafa labarin kamar haka:
"Wata budurwa mai suna Blessing da take zaune da wata kawarta mai suna Olamide a dakin Fagunwa sun samu sabani da kawartan akan wani agogon hannu da ya bace. Olamide dai tana zargin cewa Blessing ce take yi mata sata, hakan ya saka ta koreta daga dakin, sannan kuma ta yi mata gargadi mai tsawo cewa kada ta sake tayi wasa aljanu 'yan ruwa, inda ta bayyana mata cewa tabbas ita aljanar ruwa ce."
Wannan magana da tayi ya jawo hankalin 'yan makarantar da yawa, inda suka bayyana cewa dama can suna zargin cewa ita ba mutum ba ce, sun sau daya kawai take yin wanka a rana, kuma gadonta kullum a jike yake da ruwa, sannan tana tashi cikin dare ta dinga zuba ruwa a kanta da kuma kafarta, sannan kuma tana da wata sarka da kullum take bautawa da safe.
"Wannan magana da tayi ta sanya dalibai 'yan dakinsu suka fito da ita ta karfin tsiya daga dakin, duk kuwa da ta gaya musu cewa ita ba mutum bace.
"Wannan abu da aka yi mata ya sanya ta bayyana musu cewa, wannan sarka da aka dauke mata ita ce take kareta daga komawa kifi. Bayan ta bayyana haka daga baya an sanya wasu manyan mutane sun zo sun fita da ita daga cikin makarantar."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng