An nada diyar Danjuma Goje mukamin kwamishina a gwamnatin jahar Gombe

An nada diyar Danjuma Goje mukamin kwamishina a gwamnatin jahar Gombe

Majalisar dokokin jahar Gombe za ta tantance diyar tsohon gwamnan jahar, Sanata Danjuma Goje wanda gwamnan jahar Muhammadu Inuwa Yahaya ya aika musu da nufin nadata mukamin kwamishina.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito majalisar za ta tantance diyar tsohon gwamnan, Dakta Hussaina Goje ne a yau Alhamis, 24 ga watan Oktoba tare da wasu mutane guda hudu da gwamnan ya aika da sunayensu da suka hada da Adamu Dishi, Mohammad Gambo, da Usman Jahun Biri.

KU KARANTA: Hattara jama’a: Sojojin Najeriya zasu yi gwaje gwajen makamai a jahar Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba ne majalisar ta fara tantance sunayen sabbin kwamishinonin inda ta fara da Zubairu Mohammed Umar, Ibrahim Dasuki Jalo, Mohammed Magaji, Yahaya Mijinyawa, Ibrahim Alhassan, Aishatu Umar Maigari da Julisu Ishaya.

Shugaban kwamitin tantancewar, Shuaibu Adamu Haruna ya bayyana cewa suna sa ran kammala tantance sabbin kwamishinonin cikin kwanaki uku, faraway daga Laraba, Alhamis zuwa Juma’a.

Sai dai majalisar dokokin jahar a karkashin jagorancin kaakakin majalisar dokokin jahar, Abubakar Sadiq Ibrahim ya umarci Dakta Aishatu, Magaji Gettado da Julius Ishaya dasu rusuna ne kawai su wuce.

Majalisar ta umarce mutanen su rusuna su tafi ne sakamakon Magaji Gettado ya taba zama dan majalisar dokokin jahar, yayin da Ishaya Julius kuma shine mataimakin shugaban jam’iyyar APC yayin da Aishatu Maigari ta kasance guda daga cikin mata uku da gwamnan ya tura.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Adamawa Umar Fintiri ya aika da sunan mutane 23 da yake muradin nadawa mukamin kwamishina ga majalisar dokokin jahar domin ta tantancesu, daga cikinsu har da dan Atiku Abubakar, Adamu Atiku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel