Gaskiyar dalilin da yasa muke gudanar da kare kasafin kudi cikin sirri – Majalisar wakilai
- Femi Gbajabiamila, Kakakin majalisar wakilai, ya bayyana dalilin da ya sa wasu kwamitocin majalisar ke gudanar da muhawarar kare kasafin kudi cikin sirri
- Ya ce wasu kwamitin sun zabi gudanar da kare kasafin kudinsu cikin siri saboda wasu dalilai da ke da nasaba da tsaro ko kuma ra’ayin kasar
- Gbajabiamila yace majalisar na kokarin kammala kare kasafin kudin zuwa ranar 29 ga watan Oktoba da aka diba mata a matsayin wa’adi ba tare da ta tsallake tsari ba
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa wasu kwamiti na gudanar da muhawarar kare kasafin kudi ne cikin sirri ne saboda hali na tsaro.
Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba lokacin da ya ziyarci kwamitoci daban-daban a yayin muhawarar kare kasafin kudinsu na 2020 tare da hukumomin ma’aikatu.
Ya ce wasu kwamitin sun zabi gudanar da kare kasafin kudinsu cikin siri saboda wasu dalilai da ke da nasaba da tsaro ko kuma ra’ayin kasar.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin Nasarawa ta tabbatar da zababbun kwamishinonin Gwamna Sule
Kakakin yace majalisar na kokarin kammala kare kasafin kudin zuwa ranar 29 ga watan Oktoba da aka diba mata a matsayin wa’adi ba tare da ta tsallake tsari ba.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng