Kudin shiga: Ya zama dole mu kara kokari a Najeriya – Inji Zainab Ahmed
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna cewa ta na cigaba da harin wasu sababbin dabarun samun kudi domin aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin 2020 da ake harin batar da tiriliyan 10.
A jiya, gwamnatin kasar ta bayyana cewa ya zama dole a buda wuta wajen neman kudi ta sauran hanyoyin duk da za a same su idan har ana so a cin ma burin da ke cikin kundin kasafin badi.
Zainab Shamsuna Ahmed ta kyankyasa wannan ne a lokacin da ta kare kasafin kudinta Ranar 23 ga Oktoba a gaban majalisar wakilai a Abuja inda tace su na neman kudi a wajen man fetur.
Shamsuna Ahmed ta na cewa: “Mu na fama ne da matsalar samun kudin shiga; kokarin tatsar kudinmu 58% ne rak. Don haka mu ka tsara hanyar kara samun kudi a farkon shekarar nan.”
KU KARANTA: Buhari ya amince da wasu nade-nade a Ma'aikatar jiragen sama
Babbar Ministar kudi da kasafin kasar tace dole a yi garambawul a game da yadda gwamnatin tarayya za ta rika samun wasu kudi daban da ba ta bangaren mai ba, inda ta tabo batun aron kudi.
“Akwai bukatar mu samu damar inganta samun kudin shiganmu. A matsayinmu na kasa, dole Najeriya ta samu dukiyar da za ta gina abubuwan more rayuwa da ayyukan a zo–a gani.” Inji ta.
A cewar Ministar abin da Najeriya ta ke samu na kudin shiga kashi 8% ne na jimillar karfin arzikinta na GDP. Haka zalika duk bashin da Najeriya ta ke ci, bai kai 50% na arzikin kasar ba.
Daily Trust ta rahoto cewa wasu Sanatoci su na ganin bai kamata gwamnati ta cigaba da neman aron kudi ba. Ministar kudin kuwa ta na ganin har yanzu ba ta haura malejin cin bashin na ta ba.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng