An nada Sa'a Ibrahim sabuwar shugaba ta kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya

An nada Sa'a Ibrahim sabuwar shugaba ta kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya

An zabi shugabar gidan talabijin na ARTV da ke Kano, Hajiya Sa’a Ibrahim, a matsayin sabuwar shugabar Kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin ta kasa, BON (Broadcasting Organisation of Nigeria).

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, Hajiya Sa'a ta kasance sabuwar shugabar BON a taron kungiyar karo na 72 da aka gudanar biyo bayan rashin tantantar takara da abokin hamayyarta yayi.

An ruwaito cewa, Hajiya Sa'a wadda ta kasance 'yar asalin karamar hukumar cikin birnin Kano wato Kano Municipal sanadiyar fitowar ta daga unguwar Magashi, ta yi nasara a kan shugaban kamfanin yada labarai na jihar Adamawa, ABC, Yusuf Nadabo.

Gabanin wannan zabe na yanzu, shugabar ta kamfanin ARTV ta kasance tsohuwar mataimakiyar shugaban Kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin ta kasa.

Da take gabatar da jawabanta na farko yayin karbar akalar jagoranci, Hajiya Sa'a bayan yabawa dukkanin mambobin kungiyar duba da yadda ka gudanar da zabenta ba tare da samun wata tangarda ba, ta sha alwashin damawa da dukkanin mambobin kungiyar domin kawo managarcin sauyi na ci gaba.

KARANTA KUMA: Tsawa ta hallaka shanu 8 a jihar Ondo

Ta kuma cewa za ta yi iyaka bakin kokarinta wajen samar rassan kungiyar BON a dukkanin jihohin da ke fadin Najeriya gabanin wa'adinta ya kawo karshe.

A yayin da waiwaye ya tabbatar da cewa an kafa kungiyar BON a shekarar 1973 a matsayin hadin gwiwar kafofin yada labarai na masu zaman kansu da kuma na gwamnati, za'a gudanar da taronta na gaba a birnin Kanon Dabo.

BON tana da mambobi fiye da 100 tare da mallakar Gidajen Rediyo da na Talabijin fiye da 250 a fadin Najeriya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel