Tsawa ta hallaka shanu 8 a jihar Ondo

Tsawa ta hallaka shanu 8 a jihar Ondo

Akalla kimanin shanu 8 mallakin wasu makiyaya na Fulani sun halaka yayin da tsawa da fada kansu da Yammacin ranar Talata cikin yankin Ikare na karamar hukumar Akoko ta jihar Ondo a Kudancin Najeriya.

An tattaro cewa, shanun takwas sun yi gamo da ajali a bisa tudun wani dutse da ke yankin Oyinmo na karamar hukumar Akoko yayin da wasu makiyaya biyu suka kado su kiwo, wanda suka arce bayan aukuwar lamarin.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, kiwon shanu da makiyaya na Fulani ke yi a yankunan ya zamto wata mummunar al'ada da ke ci gaba da haddasa rikici a kai a kai a tsakanin su da manoma.

Wannan mummunan lamari na zuwa ne makonni kadan da aukuwar makamacinsa, inda akalla kimanin shanu 36 mallakin wani makiyayi na Fulani suka halaka yayin da tsawa da fada kansu cikin yankin Ijare na karamar hukumar Ifedore ta jihar Ondon.

Legit.ng ta ruwaito cewa, makiyaya sun kada shanunsu yankin wani jeji da ake kira Oke Owa, wanda ya kasance haramtaccen wurin kiwo sai dai ga Sarakuna kadai sakamakon tsarki da wurin yake da shi a fahimtar al'adu na al'ummar yankin.

Babu shakka tsawa ta afka kan shanu kimanin 36 a jejin Oke Owa inda nan take suka mutu murus babu ko shuruwa, ganin wannan abun al'ajabi ya sanya makiwatan shanun suka arce da kafafunsu.

Duk da cewa babu rai daya na mutum da ya salwanta, rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari ya kada hantar al'ummar yankin tare da jefa su cikin zulumi, da ya sanya kowanen su ya sake shiga taitayin sa.

KARANTA KUMA: Za'a kashe mutane 16 saboda kisan daliba a kasar Indiya

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ondo, Mr Femi Joseph, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari da cewa, kudira ce kawai ta Ubangijin halittu da sai dai a rungumi kaddara.

Sai dai wani dan gargajiya a yankin, Wemimo Olaniran, ya ce shanun sun halaka ne a sanadiyar ketara wa ta cikin tsarkakken wuri da ya haramta ga dukkanin wani mai rai face Sarki.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel