Dalilan da ya sa Askarawa ke tsaron limamai a Masallacin Makkah

Dalilan da ya sa Askarawa ke tsaron limamai a Masallacin Makkah

A wata sanarwa da masallantan Haram na birnin Makkah da Madinah da ke Saudiyya ya wallafa a shafinsa na zauren sada zumunta, ya fayyace dalilan da suka sanya Askarawa ke tsaron Limaman masallatan a yayin jagorancin kowace Sallah.

Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, hakan na zuwa ne a sanadiyar yawan tambayoyi da jama'a ke yi na neman masaniyar dalilan da suka sanya Askarawa ke bayar da kariya ga limaman mafi kololuwar masallatan alfarma biyu da ke kasar mai tsarki.

Sanarwar da shafin ya wallafa ya fayyace dalilai, inda ya hikaito yadda a shekarun baya limamai ke shiga masallatan ba tare da rakiyar Askarawa ba. Sai dai lamarin ya sauya zani bayan faruwar wasu ababe da suka sanya aka dauki mataki babu shiri.

Shafin na masjidul haramain a sanarwarsa ya shimfida wasu manyan dalilai har uku da suka sanya hukumar masallatan biyu suka dauki matakai na bai wa limamai kariya kamar haka:

  1. Akwai lokacin da wani mutum ya tunkari Sheikh Ali Al Hudaify yana ihu a dai-dai lokacin da limamin ke jan sallar Asuba a shekarar 2015.
  2. Haka kuma wani mutum ya ture Sheikh Juhany, sannan mutumin ya fara ihu a makirifo a lokacin da limamin ke jan sallar Azahar a shekarar 2011.
  3. Yayin da wani mutum ya yi yunkurin soka wa Sheikh Sudais wuka a lokacin da yake zaman tahiya a masallacin Ka'aba da ke Makka a karshen shekarun 2000.

Hakazalika yaduwar kafofin yada labarai na zamani da kuma zaurukan sada zumunta a duniya, ya sanya mutane da dama sun wayi fuskokin limaman koda kuwa sun kasance a cikin taron jama'a, lamarin da ya sa Askarawa suka zamto dogaransu domin gudun sake faruwar makamantan abubuwar da suka wakana a baya.

KARANTA KUMA: Muradin inganta jin dadin rayuwar al'umma ya sanya harkokin kasuwanci na ke ci gaba da habaka - Dangote

Baya ga haka kuma, mutane masu sauke farali yayin aikin Hajji ko Umarah, sun kan yi yunkurin rungumar limaman a sanadiyar kamuwa da shaukin ganin su, inda wasu kan yi kokarin taba gemunsu domin samun tabarraki.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Askarawan da ke bai wa limaman kariya yayin da suke jagorancin sallah, su na yin ta su sallar ne bayan an kammala sallar jam'i.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel