Trudeau ya sake lashe zaben shugabancin kasar Canada
Shugaban kasar Canada, Justin Trudeau, ya sake lashe zaben kasarsa a karo na biyu, a wani zabe da aka gudanar wanda jaridar BBC ta ce ya sha da kyar, inda a yanzu zai kasance firaiministan gwamnatin 'yan tsiraru.
Gabanin babban zaben kasar, an kiyasta cewa jam'iyyar shugaba Trudeau ta Liberals, za ta samu rinjaye da kujeru 157 a majalisar tarayyar kasar, wanda a yanzu ana hasashen zai fuskanci kalubale wajen zartar da dokoki a wa'adin gwamnatinsa na biyu.
Da ya ke kana taka ne kuma Allah na tasa, an yi tsammanin cewa jam'iyyar adawa ta Conservatives za ta samu kuri'u mafi rinjayen da aka kada, sai dai hakan bai sa sun samu rinjayen kujeru a majalisar kasar ba.
A sakamakon zaben kasar daaka fitar a daren ranar Litinin da ta gabata ya nuna cewa, kujerun da jam'iyyar ra'ayin rikau ta NDP, (New Democratic Party) ta samu sun ragu, sai shugabanta Jagmeet Singh, zai iya kasancewa mai karfin fada a ji.
Haka kuma an yi hasashen jam'iyyar NDP za ta samu kujeru 24 cikin 338 na majalisar dokokin kasar.
KARANTA KUMA: An daure Basudane tsawon shekaru biyu da laifin fataucin muggan kwayoyi a Najeriya
Jam'iyyar 'yan awaren Quebec ta Bloc Québécois, wadda ta yi takararta kadai a lardin da ta ware kanta, ta tsinana abin zo a gani yayin da ta samu kujeru 32 fiye da goman da ta samu a zaben shekarar 2015
An tattaro cewa, gwamnatin shugaban kasa Trudeau ta fuskanci matsananciyar suka gami da caccaka a tsawon shekaru hudun baya da ta shafe a karagar mulki, biyo bayan kashi a gidin da ya yi wa gwamnatinsa dabaibayi.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng