'Yan fansho a Kano sun tanka wa gwamnati, sun yi tone-tone

'Yan fansho a Kano sun tanka wa gwamnati, sun yi tone-tone

Shugaban kungiyar 'yan fansho na kasa reshen jihar Kano, Alhaji Salisu Ahmed ya ce a kalla mambobinsu 3,000 da suka yi ritaya daga 2016 zuwa 2018 har yanzu ba su samu garatuti din su ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya ziyarci tawagar 'yan kungiyar da suka kai wa Kakakin majalisar jihar Kano, Alhaji Abdulazeez Garba-Gafasa ziyarar ban girma.

Ya ce, "Mambobin mu fiye da 3,000 da su kayi ritaya daga 2016 zuwa 2018 ba su samu ko kwabo ba cikin kudinsu na garatuti. Hakan ya janyo musu wahalhalu da yawa wasu ma cikinsu sun mutu ba tare da samun hakokinsu ba.

"Abin na damunmu kuma ya zama dole mu fadi bayyana halin da wasu da yawa cikin mu ke ciki da kallubalen da suke fuskanta kan rashin biyansu hakokinsu.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

"Saboda haka muna kira ga Kakakin majalisa ya saka baki cikin batun domin a kawo karshen wahalhalun da mambobin mu ke fuskanta."

Ya yi bayyanin cewa an kafa kwamitocci biyu kan batun 'yan fansho a jihar kuma sun kammala binciken sun mika rahotonsu amma gwamnatin jihar ba ta dauki mataki ba.

A jawabinsa, Kakakin Majalisar ya shawarci kungiyar su gana da Gwamna Abdullahi Ganduje a kan batun domin su sake gabatar masa da koken su.

Ya kuma basu tabbacin cewa majalisa za tayi duk mai yiwuwa don ganin an magance matsalolin da suke fama da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel