'Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya 4 a Borno

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya 4 a Borno

Akalla sojojin Najeriya hudu da wani dakarun sa kai guda daya sun riga mu gidan gaskiya yayin wani artabu da mayakan kungiyar ta'adda ta IS a ranar Asabar cikin jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kamar yadda jaridar The Punch ta kalato rahoto daga kafar watsa labarai ta AFP a ranar Lahadi, bakin gumurzu ya auku yayin da 'yan ta'adda suka yi wa tawagar dakarun sojin Najeriya kwanton bauna daura da kauyan Jakana, wanda ke nisan mita duba 42 da birnin Maiduguri.

Rahotanni sun bayyana cewa, da yawan dakarun soji sun jikkata a yayin da kuma mayakan IS suka tarwatsa motocin yaki hudu na dakaru.

Cikin sanarwar da rundunar dakarun Najeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an samu nasarar hallaka mayakan IS bakwai yayin da takwas kuma suka jikkata.

Kakakin rundunar sojin, Kanal Aminu Iliyasu, shi ne ya bayar da tabbacin hakan yayin ganawa da manema labarai a Jakana.

Jakana wani kauye ne da ke mararraba da birnin Maidugurin Borno da kuma birnin Damaturu na jihar Yobe, inda a watan Yulin da ya gabata rayukan dakarun sojin Najeriya shida suka salwanta yayin gumurzu da 'yan ta'adda.

KARANTA KUMA: Gobara ta kona shaguna 300 a kasuwar Benin

A tsawon shekaru kimanin goma da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta daura damarar ta'addanci a tsakanin kasashen Nijar, Chadi da kuma Najeriya, rayukan mutane fiye da 35,000 sun salwanta yayin da fiye da mutum miliyan biyu suka tsere daga muhallansu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel