Sojoji sun harba wa mayakan Boko Haram Bam, 7 sun mutu

Sojoji sun harba wa mayakan Boko Haram Bam, 7 sun mutu

Rundunar sojin Najeriya, ta sanar da cewa, 'yan ta'adda 7 ne suka kurmushe sakamakon bam din da ya tashi dasu.

Rundunar sojin ne suka dasa abun mai fashewa a dajin Lamba da ke kan titin Jakana-Mainok dake Barno.

Shugaban yada labarai na rundunar, Col. Aminu Iliyasu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi. Ya kara da cewa, 'yan ta'adda 8 ne suka rasa kafafunsu sakamakon tashin bam din.

Ya ce: "Abinda ya faru na bayyana dabarun sojin. Mota mai kira Toyota ta 'yan ta'addan ta tarwatse sakamakon abu mai fashewa da sojin suka dasa."

Iliyasu ya kara da bayyana cewa, wani dan sumogal da ya kware da kawo busasshen kifi daga yankin tafkin Chadi son siyarwa an cafkeshi.

Ya ce, "An cafke mutane hudu da ake zargi tare da buhuna 16 na busasshen kifi. A kuma wani cigaba, rundunar sojin ta tare ababen hawa 10 dankare da busasshen kifi a Bukarti, a karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe akan hanyar zuwa Hadejia ta jihar Jigawa."

"A hakan kuma an cafke mutane 18 da ake zargi wadanda suka hada da direbobi, kanikawa da sauransu," in ji shi.

Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa, an cafke wani Musa Ishaku da katin shaidar ma'aikatan kwastam na bogi wanda yake amfani dashi wajen yaudarar jami'an tsaro.

A jihar Kaduna kuwa, rundunar sojin ta ceto dalibai 4 daga 'yan ta'addan suka save a kauyen Gurmi dake karamar hukumar Chikun ta jihad bayan musayar wuta da suka yi da 'yan ta'addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel