Atisayen rundunar soji: Mahaifiyar Nnamdi Kanu ta mutu
Sally Kanu, mahaifiyar shugaban 'yan kungiyar aware ta 'yan asalin kabilar Igbo (IPOB), Nnamdi Kanu, ta mutu.
Mista Kanu ne da kansa ya sanar da mutuwar mahaifiyarsa a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa ta mutu ne ranar 30 ga watan Agusta bayan ta sha fama da doguwar jinya a kasar Jamus.
Kazalika, ya alakanta mutuwar mahaifiyar tasa da gwamnati, inda ya dora alhakin silar mutuwar ta a kan kutsen da dakarun soji suka yi zuwa cikin gidansa da ke Umuahia, jihar Abia, a watan Satumba na shekarar 2017.
"Ta kamu da rashin lafiyar ajali ne bayan ta ga yadda gwamnatin tarayya ke kashe mata 'ya'ya a kan idonta, yau ga shi mun rasa ta," a cewar Kanu.
Sai dai, ya lashi takobin cewa mutuwar mahaifiyarsa ba zata sanyaya masa gwuiwa ba wajen cigaba da gwagwarmayar neman kafa kasar Biafra ta 'yan kabilar Igbo.
"Na sha fada a baya cewa zan iya sadaukar da komai domin dalilin Biafra, yau ga shi na sadaukar da mahaifiyata. Babu abinda zai dauke mana hankali, za mu cigaba da nema wa mutanen mu 'yanci," a cewarsa.
DUBA WANNAN: Amarya ta fadi sumammiya ranar biki bayan ta gano wani boyayyen sirri a kan angonta
Shugaban na IPOB ya bayyana cewa mutuwar mahaifiyarsa ba ta hana shi kai ziyara ofishin majalisar dinkin duniya ba da kuma gudanar da sauran al'amuran kungiyarsa ba, a saboda haka mutuwar mahaifiyarsa bata dusashe karkasashin da ke cikin zuciyarsa a kan IPOB ba.
A shekarar 2017 ne dakarun sojin Najeriya suka kai wani samame gidan Mista Kanu da ke Umuahia yayin da yake cigaba da tara mutane domin cigaba da zanga-zangar neman kafa kasar Biafra, duk da yin hakan ya saba da sharadin bayar da belinsa.
Babu wanda ya san inda iyayen Kanu suke kafin ya sanar da mutuwar mahaifiiyarsa a ranar Lahadi.
Shi kansa Kanu an neme shi an rasa bayan samamen da sojojin suka kai gidansa kafin daga bisani a gan shi a kasar Isarel bayan shekara guda.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng