Amarya ta fadi sumammiya ranar biki bayan ta gano wani boyayyen sirri a kan angonta

Amarya ta fadi sumammiya ranar biki bayan ta gano wani boyayyen sirri a kan angonta

Wata ma'abociyar amfani da dandalin sada zumunta ta bayar da wani labari mai cike da ban tausayi da mamaki da ya faru a kan 'yar uwarta.

Matar mai suna Olamipos-tabiti a dandalin sada zumunta na Tuwita ta yi ikirarin cewa 'yar uwarta ta fadi sumammiya ranar da ake bikinta bayan matar mutumin da zata aura ta ziyarce ta da safiyar ranar Asabar domin sanar da ita cewa angonta na da aure.

A cewar Olamipos-tibiti, matar sabon angon ta ziyarci amaryar ne a lokacin da ta kammala shiri tsaf tana jiran angonta domin su tafi wurin shagalin biki, kuma tana sanar da ita cewa ita ce matar angon ta farko, sai kawai ta yanke jiki, ta fadi sumammiya.

Mai bayar da labarin ta cigaba da cewa, mutumin ya sanar da amaryar da zai aura cewa ya taba yin aure amma fa matar ta mutu, kuma har hotonta ya nuna mata.

Kazalika, ta bayyana cewa amaryar da angon sun hadu ne a Coci, a saboda haka sun yi neman aure mai tsafta, bisa tarbiyar addini.

Wannan ne dalilin da yasa sabuwar amaryar bata shiga jikin mutumin sosai ba domin sanin dukkan halin da yake ciki, sannan kuma gashi aiki ne ya kawo shi garin su amaryar daga garinsa na haihuwa.

DUBA WANNAN: An gano barnar da Zaki ya tafka a gidan 'Zoo' na Kano kafin a kama shi

Amaryar, ma'aikaciyar banki ta shafe kusan watanni biyu zuwa uku tana shirin ranar bikinsu, don har bashin kudi bankin da take aiki suka bata don ta yi shagulgulan biki ba tare da matsi ba.

Ana zargin cewa, mutumin mai shekaru 40, na son kara aure ne saboda bai samu haihuwa ba da natarsa ta farko.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba, kuma har zuwa safiyar ranar Lahadi, 20 ga wata, amaryar na kwance a asibiti, inda ake duba lafiyarta sakamakon faduwar da ta yi a sume da safiyar ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel