Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara

Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara

- An kama tsohon gwamnan ne da misalin karfe 1 na ranar yau Juma'a a gidansa da ke titin Nagogo da ke Kaduna

- Ana zargin tsohon gwamnan ne tare da wasu 'yan siyasa hudu da karabar N450m daga tsohuwar minstar man fetur akan zaben 2015

Jami'an hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmuda Shinkafi.

Jami'an hukumar sun tsinkayi gidan tsohon gwamnan ne dake titin Nagogo da ke Kaduna wajen karfe daya na ranar yau Juma'a inda suka yi awon gaba dashi.

KU KARANTA: Hoton wani matashin mawaki da budurwarsa sun jawo cece-kuce a tuwita

Wata majiya daga iyalansa, wacce ta bukaci a boye sunanta ta tabbatarwa da jaridar Daily Nigerian zancen kama tsohon gwamnan.

Ya ce, iyalan Shinkafi basu san inda aka yi dashi ba.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar EFCC din, yace yana bukatar lokaci don tabbatar da hakan kafin ya maida martani. "Zan tabbatar kafin in dawwo gareku," in ji shi.

A ranar Alhamis ne hukumar EFCC din ta kara mika shaidu uku gaban kotun akan shari'ar tsohon ministan kudi, Bashir Yuguda, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmuda Aliyu Shinkafi, Aminu Ahmed Nahuche da Ibrahim Mallaha a gaban mai shari'a Jastis Fatima Aminu ta babbar kotun tarayya dake Gusau.

Ana zargin su hudun da karbar naira miliyan dari hudu da hamsin daga tsohuwar ministar man fetur, Deizani Alison-Madueke don yakin nemna zaben 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel