An gurfanar da wani dan shekara 60 bayan ya yaudari wata bazawara da alkawarin aure

An gurfanar da wani dan shekara 60 bayan ya yaudari wata bazawara da alkawarin aure

Wani mutum mai shekara 60, Mista Charles, a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Ikeja, Lagas kan zargin damfarar wata mata N150,000 da muhimman kayayyaki da ya kai N627,000 kan yaudarar cewa zai aure ta.

Charles, wanda ya kasance mara aiki na fuskantar tuhume-tuhumen karban wadannan kayayyaki ta hanyar yaudara da sata.

Dan sanda mai kara, Sgt. Chekube Okeh ya fada ma kotu cewa wanda ake karan ya aikata laifukan wani lokaci a watan Oktoba 2017 a Igando, Lagas.

Okeh ya bayyana cewa mai karar, wacce ta kasance bazawara yar Shekara 50, ya yaudareta sannan yayi alkawarin aurenta.

“Wanda ake karan ya karbi N150,000 daga hannun matar sannan yayi alkawarin biyanta, ya kuma karbi dakardun filin ta da ya kai N627,000,” inji shi.

Okeh yayi bayanin cewa mai laifin ya ki aurenta kamar yadda yayi alkawari, sannan ya ki biyanta kudin da ya karba hakazalika ya ki dawo da takardun.

KU KARANTA KUMA: Kai rayayyen gwarzo ne, Buhari ga Gowon yayinda ya cika shakara 85 a duniya

Sai dai wanda ake karan ya ki amsa laifin.

Alkalin kotun, Misis A.O Akinde, ya bayar da belinsa kan N100,000 tare da wadanda za su tsaya masa mutum biyu.

Akinde ya dage zaman zuwa ranar 30 ya watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel